Direban NCDC ya kamu da cutar Korona - Gwamna Sule

Direban NCDC ya kamu da cutar Korona - Gwamna Sule

- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya tabbatar da samun karin mutum daya da ya harbu da cutar korona a jihar

- Kamar yadda gwamnan ya bayyana, wanda ya sake kamuwa da cutar a jihar direban hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ne na jihar

- An tabbatar da cewa direban NCDC din ya kamu da cutar ne a yayin da yake kaiwa da kawowa da samfur din masu cutar daga Nasarawa zuwa Abuja

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce jihar ta samu karin mutum daya da ke dauke da cutar Korona. Hakan ya kai masu dauke da cutar a jihar zuwa 12.

Sule ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga taron jami'an tsaro a ranar Talata a garin Lafia.

Gwamnan ya ce, wanda ya sake kamuwar direban hukumar kula da cutuka masu yaduwa ne wanda ke dibar samfur daga jihar zuwa hukumar da ke Abuja.

Ya ce direban na zama a karamar hukumar Karu ne da ke jihar kuma an gano yana dauke da cutar a ranar Talata.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, Gwamnan ya ce an mika mara lafiyar zuwa cibiyar killacewa da ke asibitin tarayya da ke Keffi.

Direban NCDC ya kamu da cutar Korona - Gwamna Sule

Direban NCDC ya kamu da cutar Korona - Gwamna Sule. Hoto daga BBC
Source: UGC

DUBA WANNAN: Fargaba a Jigawa yayin da mutum 100 suka mutu cikin kwana 10

Gwamnan ya bayyana cewa, dukkan majinyatan cutar na samun taimakon likitoci ne a asibitin kwararru na Dalhatu Araf da kuma asibitin tarayya da ke Keffi.

Ya kara da cewa, gwamnatin ta samu tallafin kayan kariya 6,000, takunkumin fuska 50,00 da kuma takunkumin fuska wanda 'yan bautar kasar jihar suka hada musu.

Ya yi kira ga jama'ar jihar da su kiyaye dukkan umarnin gwamnati a kan annobar COVID-19 don kawo karshenta da gaggawa.

A wani labari na daban, mutane a Jigawa sun shiga fargaba a yayin da aka ruwaito cewa fiye da mutane 100 sun mutu cikin kwanaki 10 da suka shude a karamar hukumar Hadejia na jihar kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

Rahoton ya saka gwamnatin ta kafa kwamiti mai mutane biyar domin gudanar da bincike a kan dalilin mace-macen kamar yadda hukumomi suka bayar da shawara.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Abba Zakari, wanda kuma shine shugaban kwamitin kar ta kwana na COVID 19 a jihar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel