Bayan korar ma'aikata 46 a kamfanoninsa, jami'ar Atiku ta kori ma'aikata 400

Bayan korar ma'aikata 46 a kamfanoninsa, jami'ar Atiku ta kori ma'aikata 400

- AUN, jami'ar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ta kori ma'aikata fiye da 400 ranar Litinin

- Ma'aikatan da aka kora sun yi zargin cewa ba a biyasu hakkinsu da ya kamata ba duk da sun shafe fiye da shekaru 10 su na aiki a jami'ar

- Jami'ar ta ce ta na yin wasu gyare - gyare ne tare da daidaita al'amuranta domin dacewa da manufofinta

Jami'ar AUN (American University of Nigeria) mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ta kori ma'aikata fiye da 400 a ranar Litinin.

Korar ma'aikatan na zuwa ne a cikin kwanaki uku kacal bayan wani kamfanin yada labarai na Atiku mai suna 'Gotel Communications' ya kori ma'aikata 46.

A takardar korar ma'aikatan, mai dauke da sa hannun shugaban AUN, Dawn Dekle, jami'ar ta ce ba ta da bukatar aiyukan ma'aikatan da ta kora, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

Wasu daga cikin ma'aikatan da aka kora sun shaidawa SaharaReporters cewa an koresu ba tare da biyansu kowanne alawus ba duk da cewa sun shafe fiye da shekara 10 su na aiki a jami'ar.

Sai dai, Abubakar Abba Tahir, mataimakin shugaban jami'ar mai kula da hulda da jama'a, ya musanta zargin ma'aikatan.

Bayan korar ma'aikata 46 a kamfanoninsa, jami'ar Atiku ta kori ma'aikata 400
Takardar korar ma'aikata a jami'ar AUN Hoto: SaharaReporters
Asali: UGC

"Ku tambayesu su nuna mu ku takardunsu na sallama daga aiki

"Jami'ar AUN ta na daukan ma'aikata ne bisa la'akari da yawan dalibanta, hakan kuma ya zama barazana ga dorewar jami'ar a halin yanzu.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kama manyan 'yan leken asirin kungiyar Boko Harm 16, sun kashe mayaka 134

"AUN ba za ta iya cigaba da rike ma'aikatan da ba ta bukata ba, wadanda ba za su kara wata martaba ga yadda ake gudanar da jami'ar ba.

"Mahukuntan AUN sun zauna tare da gudanar da muhimmin taro a kan yadda za a cigaba da gudanar da jami'ar, yayin taron ne aka zo da tsarin daidaita sahun aiyuka da ma'aikata.

"Lokaci ne da jami'ar AUN ke yin duba tare da bullo da tsare - tsaren da za su tabbatar ta cigaba da rayuwa bisa tsari da manufofin da aka ginata a kai," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel