Dokar hukumar yaki da Coronavirus: Dino Melaye ya shigar da karar ministan Buhari da IG na Yansanda

Dokar hukumar yaki da Coronavirus: Dino Melaye ya shigar da karar ministan Buhari da IG na Yansanda

Sanata Dino Melaye ya shigar da karar kakaakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila gaban kotu kan kudurin dokar hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa, NCDC.

Hukumar NCDC ita ce hukuma daya tilo dake kan gaba wajen yaki da annobar cutar Coronavirus a Najeriya a yanzu haka, cutar da ta kama fiye da mutane 2,500 ta kashe fiye da 80.

KU KARANTA: Shugaban kasar Togo Gnassingbe ya amshi rantsuwar mulki karo na 4

Hakan ta sa kakaakin majalisa, Femi Gbajabiamila ya gabatar da kudiri a gaban majalisa da za ta baiwa gwamnati ikon amfani da duk wani gida a kasar nan don killace masu cutar.

Sai dai Dino ya kalubalanci kudurin, don haka ya maka kakaakin, ministan sharia Abubakar Malami, sufetan Yansanda Muhammadu Adamu da akawun majalisun dokoki gaban kotu.

Melaye ya shigar da karar mutanen ne a gaban babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, kara mai lamba FHC/ABJ/CS/463/2020, a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu.

Dino ya danganta kararsa ga tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya daya baiwa kowa daman mallakar kadara a ko ina a kasar, tare da yancin rayuwa da walwala da kuma kare mutunci.

Lauyan Melaye, Okoro Nkemakolam ya nemi kotun ta bayyana sassan kudurin na 3(8),5(3),6,8, 13,15,16,17,19,23,30 da 47 a matsayin karan tsaye ga yancin dan Adam a Najeriya.

Haka zalika lauyan ya nemi kotun ta dakatar da majalisar daga tafka muhawara a kan sassan kudurin dokar da suka take hakkin bil adama a Najeriya.

Sauran korafe korafen Dino Melaye su ne:

“Na san cewa sashi na 16, 17 da na 19 na kudurin zai baiwa shugaban hukumar NCDC daman bayyana wani gida ko taro a matsayin mai cunkoso ta yadda ko ba tare da umarnin kotu ba zai iya tarwatsa taron ko da da karfin tuwo kuma ya kulle gidan, wannan shiga hakkin dan Najeirya ne.

“Na sani cewa sashi na 19(5) na kudurin ya tanadi iko ga ministan kiwon lafiya ya hana ni zuwa kotu don neman hakki na, akasain yadda dokokin kare yancin dan Adam na nahiyar Afirka ta tanadar da kuma dokokin Najeriya suka tanadar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel