Ma su gudu su gudu: Bidiyon yadda jama'a su ka fece bayan wani mutum ya yanke jiki ya fadi a layin ATM

Ma su gudu su gudu: Bidiyon yadda jama'a su ka fece bayan wani mutum ya yanke jiki ya fadi a layin ATM

Jama'a sun ranta a na kare bayan wani mutum ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke amfani da na'urar ATM a wani banki a jihar Legas.

Gidan Talabijin na TVC ya rawaito cewa mutumin ya fadi, ya na numfashi sama - sama, a gaban na'urar ATM bayan layi ya zo kansa.

Jami'an tsaron bankin sun dauki mutumin zuwa cikin rumfa, kuma sun fuskanci akwai zazzabi mai zafi a jikinsa, lamarin da ya sa wasu kwastomomin bankin fecewa da gudu.

A yau, Litinin, ne umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na sassauta kulle a jihohin Lagos, Abuja da Osun ya fara aiki.

Jama'a sun yi tururuwar fitowa bayan sun shafe kusan wata guda a cikin dokar hana zirga - zirga da walwala, wacce gwamnati ta saka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta ce annobar cutar covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 170 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 12:01 na safiyar ranar Litinin, 04 ga watan Mayu, 2020.

DUBA WANNAN: Covid-19: An rufe fadar sarkin Daura bayan mutuwar matar sarki

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 170 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

39-Lagos

29-Kano

24-Ogun

18-Bauchi

15-Kaduna

12-FCT

12-Sokoto

8-Katsina

7-Borno

3-Nasarawa

2-Adamawa

1-Oyo

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Lahadi, 03 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 2558 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 400 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 87.

Alkaluman NCDC na ranar Lahadi, 03 ga watan Afrilu, sun nuna cewa an samu raguwar mutanen da annobar ta harba idan aka kwatanta da alkaluman baya bayan nan da hukumar ta fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel