Abba Kyari bai taba tuka mota ba har zuwa mutuwarsa, in ji diyarsa

Abba Kyari bai taba tuka mota ba har zuwa mutuwarsa, in ji diyarsa

Aisha, diyar Mallam Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa mahaifinta bai taba tuka mota ba har ya rasu.

A ta'aziyya mai taba zuciya da ta wallafa a jaridar ThisDay mai taken 'Mahaifina, babban abokina', Aisha ta kwatanta marigayin da mutum na gari wanda ke da gogewa mai tarin yawa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Ta bayyana cewa babban abin mamakin shine yadda bai iya tuka mota ba duk da gogewarsa a rayuwarsa.

"Wannan zai zama babban abin mamaki amma mahaifina bai iya tuka mota ba. Bai taba koya ba kuma har ya rasu," ta rubuta.

Abba Kyari bai taba tuka mota ba har zuwa mutuwarsa, in ji diyarsa

Abba Kyari bai taba tuka mota ba har zuwa mutuwarsa, in ji diyarsa
Source: UGC

Ta kara da bayyana yadda mutane da yawa basu fahimci mahaifinta ba duk da gudumawar da ya baiwa kasar nan.

"Mutane da yawa basu fahimci mahaifina ba. Hatta shekarunsa ba a fahimta ba tun da ya hau kujerar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

"Ya rasu yana da shekaru 67 amma ana yawan ruda shekarunsa da na Birgediya Abba Kyari mai shekaru 80," ta kara da cewa.

Kamar yadda yace, hukuncin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar bai taba kare kan shi daga yadda jama'a ke kalubalantarsa ba. Hakan ne yasa ya mayar da hankali wurin hidimtawa kasarsa.

"Domin ku fahimta, mahaifina yana da karfi tare da bakin kare kansa. Dalilin da yasa ya ki yin hakan kawai shine don kada hankalinsa ya dauke daga bautawa kasarsa," Aisha ta rubuta.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Ta harbi mutane 66 a Sokoto, Tambuwal ya rufe jihar, ya nemi tallafin FG

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Kyari ya rasu ne sakamakon annobar Coronavirus a ranar 17 ga watan Afirilun 2020, makonni kadan bayan an tabbatar da yana dauke da cutar ta coronavirus wacce ya samo a kasar Jamus.

Aisha Kyari wacce ta kasance babbar diyarsa ta hau kanun labarai bayan ta yi kira ga masu kalubalantar mahaifinta da su bar shi ya huta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel