Annobar covid-19 ta hallaka matar da mijinta ya shafa mata cutar a jihar Jigawa

Annobar covid-19 ta hallaka matar da mijinta ya shafa mata cutar a jihar Jigawa

A ranar Lahadi ne gwamnatin jigawa ta sanar da mutuwar mutum na biyu da annobar covid-19 ta harba a jihar.

Kafin wannan sanarwa, rahotanni sun bayyana yadda wani mutum, mazaunin unguwar Fanisau a karamar hukumar Dutse, ya mutu bayan ya kamu da kwayar cutar covid-19.

A hirarsa da gidan radiyon Freedom, kwamishinan lafiya a Jigawa, Dakta Abba Zakari, ya ce mutum na biyu da ya mutu a jihar, wata mace ce da ke zaune a karamar hukumar Miga.

Dakta Zakari, shugaban kwamitin kar ta kwana a kan yaki da annobar covid-19 a Jigawa, ya ce an kwantar da matar a asibitoci daban - daban a jihar kafin daga baya aka gano ta na dauke da kwayar cutar covid-19.

Ya kara da cewa matar ta na fama da wasu cututtukan kafin mijinta ya harbeta da kwayar cutar covid-19 bayan dawowarsa daga jihar Legas.

A kokarin da Jigawa ke yi na yaki da annobar covid-19, gwamnati jihar ta dauki jinin almajirai 679 zuwa dakin gwaji da NCDC ta amince da shi.

An dawo da almajiran jihar Jigawa ne daga wasu jihohin arewa bayan barkewar annobar covid-19.

Annobar covid-19 ta hallaka matar da mijinta ya shafa mata cutar a jihar Jigawa

Badaru Abubakar; gwamnan jihar Jigawa
Source: Twitter

Kazalika, gwamnatin Jigawa ta ce ta gano wasu almajirai kimanin 950 da ke gararamba a karamar hukumar Kazaure bayan sun shigo jihar daga jihohi daban - daban.

Gwamnatin ta ce duk da almajiran ba 'yan asalin jihar ba ne, ta killacesu tare da fara basu abinci kyauta.

A ranar Alhamis, 29 ga watan Afrilu, ne gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe wasu kananan hukumominta guda uku bayan samun bullar annobar covid-19.

DUBA WANNAN: Covid-19: Sakamakon gwajin hadiman Buhari da su ka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito

Da yake sanar da rufe kananan hukumomin guda uku, gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, ya ce an samu karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a gidan gwamnatin Jigawa da ke Dutse, babban birnin jiha.

A cewar Badaru, an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mutum mazaunin garin Gujungu a karamar hukumar Taura.

Dayan kuma da aka samu yana dauke da kwayar cutar, dan asalin karamar hukumar Birnin Kudu ne amma yana aiki a karamar hukumar Gumel, lamarin da yasa dokar kullen ta shafi kananan hukumomi uku.

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe karamar hukumar Kazaure bayan samun mutum daya da annobar cutar covid-19 ta harba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel