Gwamnatin Buhari ta samu naira biliyan 7 daga shirya jarabawar JAMB

Gwamnatin Buhari ta samu naira biliyan 7 daga shirya jarabawar JAMB

Hukumar shirya jarabawar samun gurabe a makarantun gaba da sakandari, JAMB, ta sanar da antaya zambar kudi naira biliyan 7 ga asusun gwamnatin tarayya.

Punch ya ruwaito JAMB ta bayyana kudaden a matsayin kudin da ta samu daga shirya jarabawar JAMB na shekarar 2020, daga watan Maris zuwa watan Afrilu na shekarar.

KU KARANTA: Kada ka sassauta dokar hana shige da fice sai bayan sati 2 – PDP ga Buhari

Hukumar ta ce: “Mun fara sanya naira biliyan 3.5 a asusun gwamnatin tarayya, daga bisani muka kara naira biliyan 3.5 wanda muka samu wajen sayar da lambobin PIN na JAMB, duk da gwamnati ta rage kudin sa.”

Gwamnatin Buhari ta samu naira biliyan 7 daga shirya jarabawar JAMB

Shugaban JAMB Hoto: Punch
Source: UGC

Shugaban sashin watsa labaru a JAMB, Fabian Benjamin ya bayyana cewa shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bada umarnin a cigaba da antaya ma asusun gwamnati kudi.

Kuma ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gudanar da binciken kwakwaf a asusun hukumar JAMB domin tabbatar da babu wani kumbuya kumbuya game da al’amarin kudi a hukumar.

Benjamin ya kara da cewa: “Tun da fari, shugabancin hukumar JAMB ta dauki aniyar mayar da duk wasu kudaden da bata kashe su ba ga gwamnati, hakan tasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rage farashin JAMB daga N5,000 zuwa N3,500.

“Kafin a rage kudi lambobin PIN na jarabawar, hukumar JAMB na baiwa gwamnati fiye da naira biliyan 7.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jinjina ma juriyar yan Najeriya, inda yace Najeriya za ta farfado da karfinta bayan gushewar annobar Coronavirus.

Osinbajo ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadiminsa akan watsa labaru, Laolu Akande a yayin da yake gabatar da jawabi a taron The Platform 2020.

A jawabinsa, Osinbajo ya ce: “Za mu farfado daga wannan ibtila’I da karfin mu saboda juriyarmu, da kuma karfin tattalin arziki, akwai kalubale da dama, amma kuma akwai dama sosai na sauya yadda abubuwa suke.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel