Kano: COVID-19 ce ta ke kashe mutane inji Jagoran kwamitin PTF

Kano: COVID-19 ce ta ke kashe mutane inji Jagoran kwamitin PTF

- Kwamitin Shugaban kasa ya bayyana abin da ya ke kashe mutanen jihar Kano

- Wani shugaba na kwamitin PTF ya ce cutar Coronavirus ce ta ke ta’adi a jihar

Wani jagora a cikin kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da annobar cutar COVID-19, ya bayyana dalilin da ya sa ake samun mace-mace a jihar Kano.

Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya bayyana cewa cutar COVID-19 ce ta ke kashe mutane a ‘yan kwanakin nan a jihar Kano. Nasiru Sani Gwarzo ya ce binciken da su ka yi ne ya nuna masu haka.

Kwararren likitan wanda ya na cikin masu yaki da annobar Coronavirus ya shaidawa manema labarai dazu cewa sakamakon gwajin da su ka yi ya nuna COVID-19 ta ke kashe jama’a.

Gwarzo ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, ya ce sakamakon binciken mutuwan da aka yi kwanan bayan nan, ya tabbatar cewa akwai hannun cutar COVID-19.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Yawan mace-mace ya sa Jama’a su na barin Kano

Kano: COVID-19 ce ta ke kashe mutane inji Jagoran kwamitin PTF
Binciken kwamitin PTF ya fara nuna hannun COVID-19 a mace-macen Kano
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Dr. Nasiru Gwarzo ya fadi wannan ne da ya ke magana da ‘yan jarida bayan bikin kaddamar da wani dakin gwaji da Alhaji Aliko Dangote ya gina a Kano.

A cewar Dr. Nasiru Gwarzo: “Bari in sanar da ku cewa a mafi yawan mace-macen da aka yi kwanan nan, daga gwajin da aka yi, an gano cewa cutar Coronavirus ce sanadin mutuwar.

Ya ce: “Saboda kafin cikakken rahotonmu ya fito nan da mako guda ko kuma ‘yan kwanaki, ya zama dole mutanen jihar Kano su farka daga gyangyadin da su ke yi game da annobar.”

“Ba sabon abu ba ne, kasashen Duniya irinsu Amurka, Sin, Italiya, Sifen, Ingila da Faransa da sauransu, sun yi fama da irin wannan mace-mace mai ban mamaki.” Inji Dr. Gwarzo.

Kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo Nasiru Sani Gwarzo da tawagarsa su zo jihar Kano domin su binciki abin da ya ke jawo mutuwar Bayin Allah bini-bini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel