Covid-19: Sakamakon gwajin hadiman Buhari da su ka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito

Covid-19: Sakamakon gwajin hadiman Buhari da su ka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito

Sakamakon gwajin kwayar cutar covid-19 da aka gudanar a kan wasu hadiman shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da sauran mutanen da suka halarci jana'izar Abba Kyari ya fito.

Dumbin mutane ne su ka halarci makabartar da aka binne Abba Kyari, yawancin mutanen basu saka takunkumin rufe fuska ko safar hannu ba a matsayin matakin kare yaduwar annobar cutar covid-19.

Akwai fargabar cewa jama'ar sun yi watsi da shawarar NCDC, lamarin da zai iya haifar da yaduwar kwayar cutar covid-19 a makabartar da jama'a su ka yi wa tsinke domin halartar binne marigayi Abba Kyari.

Har wasu manyan hadiman shugaban kasa aka hana shiga Villa bayan sun dawo daga jana'izar marigayi Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Sati biyu bayan faruwar hakan, sai ga shi hukumar birnin tarayya, Abuja, ta ce dukkan mutanen da aka killace ko aka bawa shawarar su killace kansu bayan halartar jana'izar, sun auna arziki.

A cikin sanarwar da mukaddashin sakataren ma'aikatar lafiya ta Abuja, Mohammed Kawu, ya fitar a yau, Lahadi, ya ce mutanen sun kammala sati biyu a killace, sannan sakamakon gwaji ya nuna cewa babu wanda ya kamu da kwayar cutar covid-19.

"Sashen kiwon lafiya da hidimtawa jama'a na birnin tarayya ya na mai farin cikin sanar da cewa mutanen da su ka halarci jana'izar Malam Abba Kyari sun kammala wa'adin sati biyu a killace.

"Sakamakon gwajin da aka gudanar a kansu ya nuna cewa babu wanda a cikinsu ya kamu da kwayar cutar covid-19.

"Dukkansu sun koma gidajensu wurin iyalinsu," a cewar sanarwar.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna Ali Modu ya yi wa jami'an NCDC wayo, ya sulale ya gudu don kar a gwada shi

SaharaReporters ta ce bincikenta ya gano cewa daga cikin hadiman Buhari da aka hana shiga fadar shugaban kasa akwai; Ambasada Lawal Kazaure, Yusuf Sabiu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa.

Sauran sun hada da Musa Haro Daura, dan uwan shugaba Buhari, da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro (NSA), da sauransu.

SaharaReporters ta ce an hana manyan hadiman shiga fadar shugaban kasa ne saboda yadda su ka yi watsi da umarnin nesanta da kare kai daga kamuwa da yada cutar covid-19 yayin jana'izar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng