Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19

Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19

Gwamnatin jihar Nasarawa ta rufe majalisar dokokin jihar Nasarawa tare da bulbula feshin magani bayan mutuwar mamba, Honarabul Suleiman Adamu, sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Cutar coronavirus ta kashe dan majalisar jihar Nasarawa, Adamu Sulaiman, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Sulaiman ne majinyaci na farko da ya rasu sakamakon cutar covid-19 a Nasarawa tun bayan da aka gano annobar ta shiga jihar.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da mutuwar dan majalisar a yayin da yake jawabi ga manema labarai a garin Lafia, babban birnin jiha.

A yayin sanar da inda aka kwana a kan annobar cutar a jihar, Gwamna Sule ya sanar da cewa Sulaiman ya rasu tun kafin sakamakon gwajinsa ya fito.

Ya yi bayanin cewa, bayan an samu sakamakon gwajin dan majalisar, iyalansa da wadanda ke rayuwa tare dashi duk an killacesu.

Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19
Majalisar jihar Nasarawa Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Gwamnan ya kara da cewa, an dauki jininsu tare da aikawa hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta (NCDC) domin gudanar da gwaji.

KU KARANTA: Bayanai sun fito a kan musabbabin mutuwar babban sarki a Zamfara

Kafin rasuwarsa, Sulaiman ya kasance mamba mai wakiltar mazabar jihar Nasarawa ta tsakiya a majalisar jihar.

Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19
Feshin magani a majalisar jihar Nasarawa Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19
Feshin magani a zauren majalisar jihar Nasarawa Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshi bayan mutuwar mamba daga cutar covid-19
Hotunan yadda aka kulle majalisar jihar Nasarawa tare da yin feshin magani Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Mazauna Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun bayyana damuwarsu a kan rashin sanin inda tsohon gwamnansu, Ali Modu Sheriff, ya ke.

SaharaReporters ta wallafa cewa tsohon gwamna Sheriff ya ki amincewa a gwada shi duk da sanin cewa ya yi mu'amala da manyan mutane da cutar covid-19 ta hallaka kwanan nan a jihar Borno.

Mamba a kwamitin yaki da annobar covid-19 a jihar Borno ya ce tsohon gwamnan ya na daga cikin mutanen da aka gano cewa sun yi mu'amala da marigayi Mohammed Goni, tsohon gwamnan Borno, da marigayi Alhaji Kyari Elkanemi, sarkin Bama.

Dukkan manyan mutanen biyu sun mutu ne sakamakon kamuwa da kwayar cutar covid-19.

Marigayi Goni da Elkanemi su na daga cikin mutanen da su ka halarci jana'izar mahaifin Sheriff, Galadima Modu Sheriff, wanda ya mutu a makon jiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng