Wata ma'aikaciyar banki mai juna biyu ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki

Wata ma'aikaciyar banki mai juna biyu ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki

- Wata ma'aikaciyar banki ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki

- Ma'aikaciyar bankin mai suna Taiwo na dauke da juna biyu mai watanni uku a jikinta

- Taiwo ta yi matukar girgiza da wasikar da ta sameta a ranar Asabar

Wata ma'aikaciyar banki mai juna biyu a Ketu/Ikorodu ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa ma'aikaciyar bankin ta yi matukar girgiza da wasikar da ta sameta a ranar Asabar.

Ma'aikaciyar bankin mai suna Taiwo na dauke da juna biyu mai watanni uku a jikinta.

Bankin ya bayyana cewa zai sallama wasu daga cikin ma'aikatansa sakamakon illar da annobar Coronavirus tayi musu.

An gano cewa da yawa daga cikin ma'aikatan bankin sun samu wasikar sallamarsu ne ta yanar gizo, lamarin da ya matukar girgiza su tare da saka su cikin alhini.

Wata ma'aikaciyar banki mai juna biyu ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki

Wata ma'aikaciyar banki mai juna biyu ta yanke jiki ta fadi bayan an mika mata takardar sallamar aiki
Source: UGC

Wani abokin aikin matar da ta fadi bayan samun wasikar sallamar, ya zanta da SaharaReporters a wayar tafi da gidanka.

Ya ce, "Sunanta Taiwo. A lokacin da t samu wasikar, ta fadi kasa warwas. Su biyu ne sallamar ta shafa a bankin a halin yanzu wadanda na tabbatar.

KU KARANTA KUMA: Mace-macen Kano: Allah ya yi wa tsohon Jarman Kano rasuwa

"Za mu san halin da sauran ke ciki nan da ranar Litinin mai zuwa. Taiwo na da juna biyu na watanni uku.

"A lokacin da ta samu labarin, ta fadi kasa warwas. 'Yan uwa da abokan arziki ne suka hanzarta kwasarta zuwa asibitin."

A wai labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da mutuwar wani mai jinyar covid-19 wanda ya gudu daga cibiyar killacewa bayan an dauki jininsa domin gudanar da gwajin kwayar cutar.

Marigayin wani mutum ne mai shekaru 60 da ke fama da ciwon sukari da hawan jini. Yahaya Sarki, kakakin gwamnan jihar Kebbi, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Asabar.

Sarki ya bayyana cewa kwamishinan lafiya a Kebbi, Alhaji Jaafaru Mohammed, ya sanar da hakan yayin da ya ke bayar da jawabi a kan bullar annobar covid-19 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel