Dangote ya bawa gwamnatin Kano tallafin cibiyar gwaji da babu kamarta a Najeriya
Gwamnan jihar Kano, Dakyta Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da cewa attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya bawa gwamnati tallafin cibiyar gwaji ta zamani wacce za a iya gwada mutum 400 a rana.
Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da ya ke gabatar da jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati.
A cikin wani jawabi da sakataren yada labaran Ganduje, Abba Anwar, ya fitar ya ce cibiyar ta zamani ce da za a iya gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 400 a rana daya.
Ya bayyana cewa, "a yayin da gwamnati ke kokarin samar da karin cibiyoyin gwaji, attajirin nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote zai bayar da tallafin cibiyar gwaji mai karfin iya yin gwaji a kan mutane 400.
"Wanna dakin gwaji na zamani zai iso Kano ranar Litinin."
Tun kafin bullar annobar covid-19 a Kano, Dangote ya samar da cibiyar killacewa mai daukan ma su jinya 500.
Yanzu haka akwai cibiyoyin gwaji guda biyu a Kano; daya a cikin asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da kuma ta cikin jami'ar Bayero (BUK).
Cibiyoyin biyu na gudanar da gwaji 108 a rana daya; 88 a cibiyar da ke AKTH, 20 a cibiyar da ke BUK.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da mutuwar wani mai jinyar covid-19 wanda ya gudu daga cibiyar killacewa bayan an dauki jininsa domin gudanar da gwajin kwayar cutar.
Marigayin wani mutum ne mai shekaru 60 da ke fama da ciwon sukari da hawan jini.
Yahaya Sarki, kakakin gwamnan jihar Kebbi, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a ranar Asabar.
Sarki ya bayyana cewa kwamishinan lafiya a Kebbi, Alhaji Jaafaru Mohammed, ya sanar da hakan yayin da ya ke bayar da jawabi a kan bullar annobar covid-19 a jihar.
DUBA WANNAN: Covid-19: Ku fidda ran daidaituwar al'amura a cikin shekarar nan - Shugaban NCDC
Yayin da ya ke gabatar da jawabin, kwamishinan ya ce, "mutum na biyu da annobar covid-19 ta hallaka a jihar Kebbi, wani mutum ne mai shekaru 60 da aka san shi da ciwon sukari da hawan jini.
"Danginsa sun kawo shi cibiyar daga asibitin koyarwa na jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto.
"Likitan da ke duba shi ya yi zargin cewa ya kamu da kwayar cutar, a saboda haka sai ya tuntubi kwamitin kar ta kwana na jiha a kan annobar covid-19," a cewar Kwamishinan.
Sannan ya cigaba da cewa, mutumin ya gudu don a kar a kai shi cibiyar killacewa bayan an dauki jininsa zuwa dakin gwaji a ranar 25 ga watan Afrilu.
Ya ce mutumin ya mutu washegari, ranar 26 ga watan Afrilu, a gida.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng