Dybala, Maldini, Felliani da sauran ‘Yan wasan da COVID-19 ta kama

Dybala, Maldini, Felliani da sauran ‘Yan wasan da COVID-19 ta kama

- Kusan mutum miliyan uku da rabi su ka kamu da Coronavirus a Duniya

- Cutar COVID-19 ba ta bar manyan taurari irinsu ‘yan wasan kwallon kafa ba

- Garay, Dybala, da Felliani su na cikin wadanda da cutar COVID-19 ta kama

Jaridar Punch ta fito da rahoto dauke da sunayen ‘yan wasan kwallon kafa su ka kamu da cutar.

Daga ciki akwai:

1. Callum Hudson-Odoi

A tsakiyar watan Maris aka tabbatar da cewa matashin ‘dan wasan Chelsea, Callum Hudson-Odoi ya kamu da cutar Coronavirus.

2. Ezequiel Garay

Kwanaki kungiyar Valencia ta tabbatar da cewa Ezequiel Garay ya na dauke da COVID-19. Sauran wadanda aka samu da cutar sun hada da Eliaquim Mangala.

3. Ekdal, La Gumina, Thorsby, Depaoli da Bereszynski

A kungiyar Sampodoria an samu ‘yan wasa da-dama da cutar ta kama. Daga ciki akwai Albin Ekdal, Antonino La Gumina, Morten Thorsby, Fabio Depaoli da Bartosz Bereszynski.

Haka zalika cutar ta kama wani babban jami’in kulon din mai suna Amedeo Baldari.

4. Maldini

Tsohon ‘dan wasan AC Milan, Paolo Maldini ya kamu da wannan cuta kwanaki amma daga baya ya samu lafiya. ‘Dansa ‘dan wasa Daniel Maldini shi ma ya yi jinyar cutar a Italiya.

KU KARANTA: Kasashen da su ke yin yunkurin kirkiro maganin cutar Coronavirus

Dybala, Maldini, Felliani da sauran ‘Yan wasan da COVID-19 ta kama
'Dan wasa Callum Hudson-Odoi ya kamu da cutar COVID-19 a Ingila
Asali: Getty Images

5. Luca Kilian

A cikin ‘yan wasan kasar Jamus, ‘dan wasan kungiyar Paderborn Luca Kilian ne ya fara kamuwa da Coronavirus.

6. Timo Hubers

A watan jiya sakamakon gwaji ya nuna cewa ‘dan wasan bayan Hannover, Timo Hubers ya kamu da COVID-19 bayan ya halarci wani taron biki.

7. Paul Akpan Udoh

Paul Udoh ‘dan wasa ne da ke bugawa wata karamar kungiyar kwallon kafa mai suna Pianese da ke Italiya. Ainihinsa ruwa-biyu ne; ‘dan Najeriya da kasar Italiya, ya kamu da cutar.

8. Paulo Dybala.

Tauraro Paulo Dybala ya na fama da cutar COVID-19 har yanzu bayan watanni da kamuwa da ita. Sai dai Budurwarsa ta karyata rade-radin cewa har yanzu ta na asibiti.

9. Maroune Felliani

A daf da karshen watan Maris ne aka samu labarin cewa ‘dan wasa Marouane Fellaini mai shekara 32 ya kamu da COVID-19. ‘Dan kwallon ya warke bayan kwanaki a asibiti a Sin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel