Korona ta kashe mutum na farko a Kaduna

Korona ta kashe mutum na farko a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum na farko a jihar kuma an samu karin mutum uku dauke da cutar.

Kwamishinar lafiya ta jihar, Dr Amina Mohammed Bolani ce ta tabbatar da hakan a ranar Asabar a garin Kaduna.

Ta ce mutum na farko da ya kamu da cutar na daga cikin mutum uku da aka tabbatar suna dauke da cutar na karshe a jihar, jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda kwamishinar ta bayyana, a halin yanzu jihar ta tabbatar da cewa mutum 28 ne suke dauke da cutar sannan ana jiran sakamakon samfur 350.

Ta ce da yawa daga cikin samfur din duk na almajiran da aka dawo dasu ne.

"An kammala gwajin almajirai 167 da suka dawo daga Kano kuma yawan masu dauke da cutar a jihar ya karu.

"A ranar Alhamis, mutum 28 ne aka tabbatar suna dauke da cutar.

"Karin mutum.ukun sun hada da maza biyu da mace daya," jami'ai suka ce.

Ta ce macen da ta harbu da cutar ma'aikaciyar lafiya ce.

"Daya daga cikin mazan biyu, tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda ya boye labarin tafiyar da ya yi zuwa Kano.

A karon farko: Cutar Korona ta kashe rai a jihar Kaduna

A karon farko: Cutar Korona ta kashe rai a jihar Kaduna. Hoto daga jaridar The Guardian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An kori ma'aikata 46 a kamfanin Atiku a ranar ma'aikata ta duniya

"Daga karshe an kwantar dashi a cibiyar killacewa yayin da yake fama da sarkewar numfashi.

"Ya rasu kafin sakamakon gwajinsa ya bayyana. Shine mutum na farko da ya rasu sakamakon cutar a jihar Kaduna," tace.

Jami'an sun ce an sanar da 'yan uwan mamacin kuma an birne shi kamar yadda NCDC ta gindaya.

Kwamishinar ta ce, "Bayan wannan ci gaban, jami'an kiwon lafiya sun fara feshin asibitoci biyun da mamacin ya kwanta.

"An kwashe ma'aikatan da suka duba shi tare da 'yan uwansa don killacewa."

Ma'aikatar lafiya ta jihar ta yi kira ga wadanda suka zargi suna dauke da cutar da su guji ma'amala da jama'a.

Su bi dokokin killace kai a gida tare da tuntubar jami'an kiwon lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel