COVID-19: El-Rufai ya bayyana adadin mutanen da ya harba da Korona

COVID-19: El-Rufai ya bayyana adadin mutanen da ya harba da Korona

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce mutum hudu ya harba da cutar coronavirus a jihar amma a halin yanzu duk sun warke.

El-Rufai, wanda shine mutum na farko da ya fara samun cutar coronavirus a jihar, ya bayyana wannan ne a dandali kashi na 24 wanda Fasto Poju Oyemade ya dauka nauyi.

Gwamnan ya ce a halin yanzu jihar Kaduna ta gwada mutum 400 kuma ta mallaki dakunan gwajin cutar har uku, SaharaReporters ta ruwaito.

Ya ce, "Kamar yadda na sanar a kwanaki kadan da suka gabata, mun karba almajirai 169 daga Kano kuma 21 daga cikinsu na dauke da cutar.

"Muna kokarin gwada wasu masu tarin yawa na daga almajiran da kuma jama'ar jihar."

Ya kara da cewa, "Mun yi nasarar rufe jihar gaba daya kuma cunkoso ya ragu sosai. Duk wanda ka gani da cutar a halin yanzu a jihar, shigo da ita yayi.

"Ni ne mutum na farko da na fara kamuwa a jihar. Covid-19 ba wasa bace, gaskiya ce sosai. Na samo nawa ne a Abuja kuma na harba mutum hudu wadanda a yanzu duk sun warke."

COVID-19: El-Rufai ya bayyana adadin mutanen da ya harba da Korona
COVID-19: El-Rufai ya bayyana adadin mutanen da ya harba da Korona. Hoto daga jaridar The Guardian
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

A wani labari na daban, Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya ce yadda gwamnatin tarayya ta dauka mataki a kan annobar korona bai dace ba.

Gumi kwararren likita ne wanda ya samu tattaunawa da jaridar New Telegraph a kan yadda shugaba Buhari ke kokarin sassauta dokar hana zirga-zirga a kasar nan.

An fara tambayar malamin ko akwai abinda zai ce ga wadandaa basu yadda da wanzuwar kwayar cutar ba.

Malamin ya bayyana cewa an taba irin wannan annobar a 1918 har zuwa 1920. Za a iya cewa wani karni ne ya juya don haka wata annobar ta samu duniya.

Shehin malamin ya bayyana cewa dole za a samu mace-mace amma akwai matukar amfani idan aka mutunta rayukan kowanne mutum. Kowanne rai na da amfani don haka ya kamata a kiyayesu ta hanyar rashin sassauta dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng