Mace-macen Kano: Yadda jarumin Kannywood ya yanke jiki ya fadi

Mace-macen Kano: Yadda jarumin Kannywood ya yanke jiki ya fadi

A jiya ne Allah ya karba rayuwar fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da wanke-wanke.

An yi jana'izar marigayin a safiyar Juma'a, daya ga watan Mayun 2020.

Marigayin mai kimanin shekaru 50 a duniya, ya rasu ya bar matar aure daya da yara shida. Biyar daga cikin yaran maza ne sai mace daya. Mahaifin marigayin na nan a raye.

Ubale babban jarumi ne wanda aka dade ana damawa da shi a masana'antar kuma ya bayyana a manyan fina-finai tun a shekarun baya.

A cikin manyan fina-finansa akwai 'Daham' da kuma 'Buri uku a Duniya'.

Mutuwar jarumin ta matukar girgiza abokan sana'arsa duba da cewa baiyi wata rashin lafiya ba.

Wa'adi ne kawai ya riskesa kamar yadda bahaushe ke cewa idan ajali yayi kira, ko babu shiri sai a garzaya a tafi.

Kamar yadda jaridar fim magazine ta tattauna da dan uwan marigayi Ubale mai suna Hamisu Ibrahim, ya ce rasuwar dan uwansa ta zo ne a ba-zata.

Mace-macen Kano: Yadda jarumin Kannywood ya yanke jiki ya fadi
Mace-macen Kano: Yadda jarumin Kannywood ya yanke jiki ya fadi. Hoto daga Fim Magazine
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

Dan uwan nasa ya ce rashin Ubale babban gibi ne a rayuwarsu a yayin da aka zanta dashi.

Dan uwan nasa ya ce bai yi wata jinya ba, hasalima yana zaune ne a kofar gida tare da makwabtansa sai ya tashi ya shiga gida da niyyar saka caji.

Fitowarsa daga gidan ke da wuya ya yanke jiki ya fadi inda aka gaggauta kai shi asibitin Nasarawa amma sai likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

Dan uwan nasa ya ci gaba da cewa, "Da cuta mutuwa ce, da Ubale ya dade da rasuwa don ya yi jinya a baya kamar ba zai tashi ba amma kuma sai ya samu sauki.

"Ya ci gaba da al'amuran rayuwarsa har zuwa ranar da ajalinsa ya cika."

Jarumai irinsu Ali Nuhu, Mustapha Nabraska, Sani Danja, Yakubu Muhammad, TY Shaaban da sauransu duk sun samu halartar jana'izar.

An birne jarumin a makabartar Tudun Murtala da ke Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel