COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya ce yadda gwamnatin tarayya ta dauka mataki a kan annobar korona bai dace ba.

Gumi kwararren likita ne wanda ya samu tattaunawa da jaridar New Telegraph a kan yadda shugaba Buhari ke kokarin sassauta dokar hana zirga-zirga a kasar nan.

An fara tambayar malamin ko akwai abinda zai ce ga wadandaa basu yadda da wanzuwar kwayar cutar ba.

Malamin ya bayyana cewa an taba irin wannan annobar a 1918 har zuwa 1920. Za a iya cewa wani karni ne ya juya don haka wata annobar ta samu duniya.

Shehin malamin ya bayyana cewa dole za a samu mace-mace amma akwai matukar amfani idan aka mutunta rayukan kowanne mutum. Kowanne rai na da amfani don haka ya kamata a kiyayesu ta hanyar rashin sassauta dokar.

Yace kullen zai fi inganci sannan a yi addu'ar samun riga-kafi ko kuma maganin cutar kacokan ko kuma duka biyun.

"Kowacce rai tana da muhimmanci kuma ya kamata ta samu ta tsira. Ka duba yadda shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya rasu sakamakon cutar, Babu wanda yake da tabbacin tsallake wannan annobar.

"Duk wani tunanin cewa an kawo cutar ne don rage yawan wata kabila ko addini, ba gaskiya bane," malamin yace.

Kamar yadda ya bayyana, kasa mai tsari za ta iya shawo kan wannan matsalar cikin kankanin lokaci.

Babban misali shine yadda kasar China ta shawo kan matsalar cikin kwanakin da basu wuce dari ba. Sun samu wannan nasarar ne sakamakon kulle kasar da suka yi tare da hana zirga-zirga.

COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka

COVID-19: Sheikh Gumi ya aike wa Buhari muhimmin sako a kan sassauta doka. Hoto daga BBc
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 238 sun sake kamuwa da Korona, jimillar ta haura 2,000

Amma idan aka duba yanayin mace-macen da ake samu a kassar Amurka, ya biyo bayan rashin yadda da wanzuwar cutar da kuma yadda wasu ke ta faman walwalarsu.

Babban malamin ya ce rashin wayar da kai da kuma sanin illolin da cutar za ta iya jawowa ne yasa 'yan Najeriya ke ci gaba da karya doka.

Ya kamata a ilimantar tare da wayar da kan jama'a don su gane babbar matsalar da ke tunkaro kasar nan idan ba a kiyaye ba.

Ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da abinci isasshe ga jama'a don kuwa tafiyar cutar nan ba dole ya zama da wuri ba.

Malamin ya bayyana cewa annobar na matakin farko ne kuma akwai yuwuwar mataki na gaba ya fi tsananta.

ya zargi gwamnatin tarayya da kin sauke nauyin da ke kanta a yayin da aka tambayeshi ra'ayinsa a kan sassauta dokar hana walwalar.

Ya ce jama'a na zaune a cikin yunwa da rashin abinci don haka ne yasa gwamnatin ke kokarin sakin jama'a. Ya ce wannan yunkuri ne na kashe mutane da kuma kin daukar dawainiyar da Ubangiji ya dora musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel