Hotunan sabon asibitin killace masu cutar Korona da jihar Legas ta bude

Hotunan sabon asibitin killace masu cutar Korona da jihar Legas ta bude

Gwamnatin jihar Legas ta bude sabon asibitin killace masu cutar Coronavirus a unguwar Gbagada yau Juma'a, 1 ga watan Mayu, 2020.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwoolu, da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin nan.

Yace: "Ya ku al'ummar jihar Legas, muna fadada cibiyoyin killace mutane tare da kara yawan kayayyakin asibiti."

"Mun kaddamar da cibiya killace mara lafiya a Gbagada yau kuma zamuyi amfani da shi wajen takaita yaduwar COVID19 a Legas."

Hotunan sabon asibitin killace masu cutar Korona da jihar Legas ta bude
Gbagada
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sabbin Mutane 9 sun kamu da Coronavirus a Bauchin Yakubu

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce ta fara fuskantar barazanar karancin gadajen kwantar da wadanda suka kamu da cutar Korona a jihar Legas.

Shugaban cibiyar na NCDC, Dakta Chikwe Iheakwaezu, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai da kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa na yakar cutar Coronavirus.

Jihar Legas ce jiha mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

Kawo yanzu, mutane 947 ne suka harbu da cutar a jihar, duk da cewa 187 sun samu waraka kuma an sallamesu.

Chikwe Iheakweazu ya bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa suna iyakan kokarinsu wajen ganin cewa an samar da isassun gadajen kwantar da sabbin masu cutar.

A cewarsa: "Legas kadai ce jihar da muke fama da karancin gadajen asibiti yanzu. Ba zamu gushe muna fadawa yan Najeriya gaskiya ba. Muna fuskantar barazanar karancin gadaje a Legas yanzu."

Gabanin yanzu, Asibitoci ukun da ake kwantar da masu cutar Coronavirus a jihar Legas sune IDH Yaba, asibitin koyarwan jami'ar Legas LUTH, Idi Araba; sannan cibiyar killacewar filin kwallon Onikan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel