Yanzu-yanzu: Mutum 26 sun warke daga cutar Korona a Legas, an sallame su

Yanzu-yanzu: Mutum 26 sun warke daga cutar Korona a Legas, an sallame su

- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da sallamar mutum 26 daga cibiyoyin killacewa ta jihar

- Sanwo-Olu ya bayyana cewa, mutum 26 da aka sallama sun kunshi maza 14 da mata 12, a ciki akwai bakin haure 2

- Gwamnan ya ce an sallami majinyatan ne bayan gwajinsu har sau biyu ya bayyana sun warke daga muguwar cutar

Majinyata 26 ne da suka yi jinyar cutar Korona aka sallama daga cibiyar killacewa ta jihar Legas.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Ya ce, "A yau ina farin cikin sanar da cewa jihar Legas za ta sallami mutum 26 da suka warke daga cutar Korona. Sun hada da maza 14, sai mata 12 wadanda suka kunshi mutum biyu da ba 'yan kasar nan ba.

"An sallamesu ne daga cibiyoyin killacewa da ke Yaba da na Onikan don su koma cikin 'yan uwansu."

An sallami majinyatan ne bayan gwajinsu har sau biyu ya nuna basu dauke da cutar, kamar yadda yace.

"Da wadannan ne jimillar wadanda suka warke daga cutar a jihar Legas cikin nasara suka kai 225," gwamnan.

Yanzu-yanzu: Mutum 26 sun warke daga cutar Korona a Legas, an sallamesu

Yanzu-yanzu: Mutum 26 sun warke daga cutar Korona a Legas, an sallamesu. Hoto daga Twitter
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

A wani labari na daban, Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Jama’tu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram, ya musanta rade-radin mika wuya da aka ce zai yi.

Ya ce gaba da gaba da dakarun Najeriya ko na kasar Chadi ba zai sa ya mika kansa garesu ba, kamar yadda jaridar HumAngle ta wallafa.

Ya kara da musanta rahotannin da ke bayyana cewa mayakansa duk sun kare kuma sauran duk sun nuna karaya.

A wani sautin murya mai tsayin minti takwas da dakika 22 da ya saki a ranar Alhamis, ya ce babu abinda ya faru da su kuma suna cikin koshin lafiya.

"Cewar da kuka yi kun ragargaza mu da 'yan uwanmu a Sambisa duk karya ne. Gwamnatin karya take yi wa jama'a don su so su," yace.

Shugaban 'yan ta'addan ya ce gwamnati ce ke kokarin janye hankalin mayakansa don su mika wuya a Chadi ko Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel