Yanzu-yanzu: UN da WHO sun tura jami'ai 3,000 jihar Kano

Yanzu-yanzu: UN da WHO sun tura jami'ai 3,000 jihar Kano

- Majalisar dinkin duniya tare da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta tura jami'ai 3,000 don bada tallafin gaggawa a jihar Kano

- Kamar yadda shugaban kwamitin yaki da annobar na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha ya bayyana, ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu

- Mustapha ya ce duk da akwai alhini a sakamakon da aka samu a jihar na ranar Alhamis, ya ce hakan na nuna nasara ne wurin zakulowa da killace masu cutar

Majalisar dinkin duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta tura jami'ai 3,000 jihar Kano don bada tallafi a kan annobar korona.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa a kan yaki da cutar, Boss Mustapha, ya sanar da hakan yayin jawabi a garin Abuja a yammacin Juma'a

Mustapha, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya ya ce martanin gwamnatin tarayya ya fara kawo nasara a jihar Kano.

Ya ce, "Ina son sanar da ku cewa an fara samun abinda ake so a jihar Kano tun bayan da dakin gwajinsu ya fara aiki.

"Kwamitin yakar cutar ta jihar tare da hadin guiwar kungiyarmu ta fadada yadda take ta zakulo wadanda suka yi mu'amala da masu cutar tare da killacesu.

Yanzu-yanzu: UN da WHO ta tura jami'ai 3,000 jihar Kano

Yanzu-yanzu: UN da WHO ta tura jami'ai 3,000 jihar Kano. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

"An mayar da hankali sosai wajen horar da jami'an kiwon lafiya da suka hada da likitoci, malaman jinya har da masu goge-goge ta yadda ba za su kwashi cutar ba.

"Muna kuma tsara wani salo daga fadar shugaban kasan wanda zai bada gudumawa a kowanne lokaci.

"Majalisar dinkin duniya tare da hadin guiwar kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta tura jami'ai 3,000 jihar Kano don karfafa yakar cutar a jihar da kananan hukumomi.

"Duk da yadda masu cutar a jihar ke hauhawa, amma kuma hakan na nuna matukar nasara ne ta yadda ake zakulo masu cutar tare da killacesu."

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a daren Alhamis ta bayyana cewa an samu karin mutum 80 da suka harbu da cutar a jihar Kano.

Hakan ne ya kai jimillar masu cutar zuwa 219 a jihar yayin da ko majinyaci daya ba a sallama ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel