A kwana 2 an samu masu cutar korona 118 a jihar Kano - NCDC
A cikin kwanaki biyu kacal mun ji cewa an samu sabbin mutane 118 da cutar korona ta harba a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma a Najeriya.
Alkaluman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC, sun nuna cewa an samu mutane 38 da cutar ta harba a jihar a ranar Laraba.
Haka kuma cutar ta harbi wasu sabbin mutum 80 a jihar a ranar Alhamis.
NCDC ta ce a yanzu jimillar mutanen da cutar ta kama a Kano sun kai 219 yayin da tuni mutane uku suka riga mu gidan gaskiya.
An samu karin hauhawar adadin ne sanadiyar dawo da aiki a dakin gwajin gano masu cutar a jihar da aka yi kwanaki uku da suka gabata.
Kawo yanzu babu ko mutum daya da ya warke a jihar Kano tun bayan bullar cutar karon farko a Najeriya a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Ma'aikatar lafiyar ta sanar da cewa, sabbin mutane 80 da suka kamu da cutar a Kano sun kasance cikin mutum 204 da suka kamu a duk fadin Najeriya a ranar Alhamis.

Asali: UGC
Kididdiga ta nuna cewa, kaso 71 cikin 100 na adadin mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun kasance a jihohin Kano, Legas da kuma birnin tarayya Abuja.
KARANTA KUMA: Wasu gwamnoni na siyasantar da lamarin cutar korona domin samun kudi daga gwamnatin tarayya - Dattawan Arewa
Jihar Legas na da kaso mafi yawan wadanda cutar ta kama wanda adadin su ya kai 976, sai kuma jihar Kano mai mutum 219 yayin da birnin tarayya ya biyo baya da mutum 178.
Ga jerin adadin sabbin mutane 204 da cutar ta harba cikin jihohin Najeriya:
Kano - 80; Legas - 45; Gombe - 12, Bauchi - 9; Sokoto - 9; Borno - 7; Edo - 7; Rivers -6 ; Ogun - 6; Abuja - 4; Akwa Ibom - 4; Bayelsa - 4; Kaduna - 3; Oyo - 2; Delta 2; Nasarawa - 2; Ondo - 1; Kebbi - 1.
Sanarwar da NCDC ta fitar da karfe 11.50 na ranar Alhamis da daddare, ta nuna cewa jimillar mutanen da cutar korona ta harba sun kai 1,932 a Najeriya, kuma mutum 319 sun warke yayin da mutane 58 suka riga mu gidan gaskiya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng