An kai hare-hare a kananan hukumomi uku a Katsina duk da dokar kulle

An kai hare-hare a kananan hukumomi uku a Katsina duk da dokar kulle

– Yan bindiga sun kai hare hare a wasu kanananan hukumomi uku a jihar Katsina

– Yan bindigan sun kai hare haren ne yayin da jihar ta saka dokar kulle saboda bullar COVID 19

– Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo ya tabbatar da wasu daga cikin hare hare a Mabai da Katsalle

Yan bindiga sun kai hare hare a kauyukan Mabai (Karamar hukumar Kankara), Banyan Kasuwa (Karamar hukumar Dustinma), Musawa (Karamar hukumar Musawa) a yayin da gwamnatin jihar ta sakar dokar kulle saboda COVID 19.

Kananan hukumomin Musawa da Dutsinma suna cikin kananan hukumomin da aka saka wa dokar kulle saboda bullar annobar coronavirus a yankunan.

'Yan bindiga sun hare hare a kananan hukumomi uku a Katsina duk da dokar kulle

'Yan bindiga sun hare hare a kananan hukumomi uku a Katsina duk da dokar kulle. Mallakin Hoto: Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

A garin Musawa, masu garkuwa da mutane sun sace wata matar aure mai suna Hadiza Sale tare da yaran ta biyu. Daga bisani masu garkuwa da mutanen sun sako yaran ta.

A kauyen Mabai, misalin karfe 12 na daren Laraba, Yan bindiga sun kai hari a kauyen inda suka kashe wani Sada Musa yayin da harsashi da ta kubce ta yi wa wani Karibu Mohammed rauni.

Kazalika, kwanaki hudu da suka gabata, Yan bindigan sun kai hari a kauyen Katsaalle inda wasu mutane da ba a tabbatar da sahihancin abinda suka fadi ba suka ce an kashe mutane biyu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da harin da kisar da aka yi a kauyen Mabai amma ya ce babu wanda aka kashe a kauyen Katsalle.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel