Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

- Gwamnatin tarayya ta umarci ma'aikatanta da ke a mataki na 14 zuwa sama da su koma bakin aikinsu

- Kamar yadda takardar da shugaban ma'aikatan tarayya, Dr Folashade Yemi-Esan ta fitar, ta ce ma'aikatan za su dinga aikin ranaku uku ne a mako

- A yayin da ta shawarci ma'aikatan da su kiyaye bakin da za su dinga kai musu ziyara, ta ce za a samar da kayayyakin wanke hannaye

Gwamnatin tarayya ta umarci ma'aikatan gwamnati daga mataki na 14 zuwa sama da su koma bakin aikinsu a ranar Litinin mai zuwa.

A wata takarda da shugaban ma'aikatan tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan ta fitar, ta ce an yi feshi a sakateriyar tarayyar kuma ana kokarin yi a sauran ofisoshin tarayyar.

Kamar yadda takardar ta bayyana: "Kamar yadda jawabin shugaban kasa ya bayyana na cewa a hankali kuma mataki daban-daban za a bi don sassauta dokar hana walwalar, ma'aikatan da ke mataki na 14 zuwa sama ana umartarsu da su koma aiki.

"Baya ga su, ana umartar duk masu ayyukan da ake bukata su koma bakin aiki a ranar Litinin 4 ga watan Mayun 2020 a matsayi mataki na farko.

Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati

"Ofisoshi za su bude ne sau uku a cikin sati. Za su yi aiki a ranakun Litinin, Laraba da Juma'a kuma za su dinga tashi da karfe 2 na yammacin kowacce rana."

Takardar ta kara da shawartar wadanda abun ya shafa da su kayyade yawan bakin da za su dinga karba a rana.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, za a samar da kayayyakin wanke hannu a wurare daban-daban a farfajiyar ofisoshin.

A wani labarin na daban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar da shawarwarin da kwamitin shugaban kasa a kan yi wa hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya garambawul a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ta bayar.

Rahoton da ake yi wa lakabi da rahoton Oransaye mai shafi 800 ya bayar da shawarar soke wasu hukumomi tare da gwamutsa wasu ma'aikatun gwamnati 102.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel