COVID-19: Cutar Korona ta sake kashe wani babban mutum a Kano

COVID-19: Cutar Korona ta sake kashe wani babban mutum a Kano

- A safiyar yau Alhamis ne Allah ya yi wa Rufai Abdulmalik, tsohon ma'aikacin bankin arewa da ke jihar Kano rasuwa

- Kamar yadda majiya daga iyalansa ta bayyana, marigayin ya killace kansa ne tun bayan da ya dawo daga ta'aziyyar Dr. Aliyu Yakubu na jihar Katsina wanda korona ta kashe

- A jiya Laraba ne Abdulmalik ya fara bayyana da alamun cutar, lamarin da yasa 'yan uwansa suka garzaya da shi asibiti

A safiyar yau Alhamis ne aka tabbatar da rasuwar tsohon babban manajan tsohon bankin Arewa, Rufa'i Abdulmalik. Ana zargin cutar coronavirus ce ta kashe shi.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta sanar da jaridar The Nation cewa mamacin ya cika ne a asibitin tarayya da ke jihar Kano.

Majiyar wacce ta bukaci da a rufe sunanta, ta bayyana cewa tsohon ma'aikacin bankin ya killace kansa ne tun bayan da ya dawo daga ta'aziyyar Dr Aliyu wanda ya rasu sakamakon annobar Coronavirus a jihar Katsina.

Gwamnatin jihar Katsina ce ta sanar da rayuwar Dr Aliyu Yakubu wanda siriki ne ga Abdulmalik sannan kuma dan uwansa daga gidan sarautar jihar Kogi.

COVID-19: Cutar Korona ta sake kashe wani babban mutum a Kano
COVID-19: Cutar Korona ta sake kashe wani babban mutum a Kano
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati

Majiyar ta kara da cewa, "Bayan dawowarsa daga Daura kuma ya samu tabbacin cewa cutar coronavirus ce ta kashe Dr. Aliyu, sai marigayin ya killace kansa na sama da kwanaki 14.

"Amma kuma da yammacin jiya Laraba sai muka lura da alamun cutar coronavirus a tattare dashi, lamarin da yasa muka hanzarta mika shi asibiti inda ya cika a yau Alhamis."

A yayin tabbatar da mutuwarsa, Tijjani Aliyu wanda dan uwan mamacin ne, ya ce: "Yanzu na samu labarin rasuwar Abdulmalik. A halin yanzu ina kan hanyar zuwa Ohinoyi ne don shirin birne shi.".

Wakilin Ibira na jihar Kano, Alhaji Yahaya Sadiq ya kwatanta wannan lamarin da abun alhini matuka.

Sadiq ya ce a halin yanzu ana ta shirin birne mamacin wanda ya samu shaida mai kyau daga jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel