Ban ji wata alamar ciwo a lokacin da na ke jinya ba – inji Mohammed Atiku Abubakar

Ban ji wata alamar ciwo a lokacin da na ke jinya ba – inji Mohammed Atiku Abubakar

A ‘yan kwanakin bayan nan ne Mohammed Atiku Abubakar ya warke daga cutar COVID-19. ‘Dan tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya shafe fiye da wata guda ya na jinya a Abuja.

Alhaji Mohammed Atiku Abubakar ya shaidawa VOA Hausa cewa har ya samu lafiya bai ji ko daya daga cikin alamun Coronavirus kamar su mura, tari ko ciwon zazzabi, a jikinsa ba.

Mohammed Atiku Abubakar ya kuma yabawa kokarin gwamnatin kasar wajen kula da wadanda su ka kamu da COVID-19. Atiku ya na cikin wadanda su ka fara kamuwa da cutar a kasar.

Atiku ya ce har ya samu sauki, sisin kobo bai yi kuka daga aljihunsa ba, domin gwamnati ce ta ke daukar nauyin kula da maras lafiya. Matashin ya yi jinya ne a Gwagwalada, birnin tarayya.

‘Dan tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya ce ya nuna ‘yar fargaba kadan musamman a farkon lokacin da ya ke jinya, hakan ya bayu ne zuwa ga cewa ya na cikin wanda cutar ta fara harbi.

KU KARANTA: Cutar COVID-19 ta harbi wani Yaron Atiku Abubakar a Garin Abuja

Da ‘yar jaridar ta VOA Hausa ta tambayesa game da zarginsa da ake yi da cewa ya je gidan rawa a lokacin da cutar ke jikinsa, Mohammed Atiku Abubakar ya ce sharri ne kurum ake yi masa.

Wannan Bawan Allah ya karyata zargin yadawa wasu wannan cuta, ya ce tun asali shi ba mutum ba ne mai shagala da zuwa gidan rawa. Ya ce ya bar wadanda su ka yi masa kage da Allah.

Har ila yau a wannan hira, yaron babban ‘dan siyasar ya bayyana cewa ba zai iya cewa ga inda ya dauko cutar Coronavirus ba. Sai dai ya yi kira ga jama’a su yi hattara da wannan annoba.

Alhaji Atiku ya ce babbar matsalar COVID-19 ita ce yadda ta ke yaduwa da wuri, sannan ba ta da magani a Duniya. Game da dadewa da ya yi ya na jinya, ya ce abin ya ba kowa mamaki.

A halin yanzu mutane fiye da 1, 700 sun kamu da Coronavirus a Najeriya. An samu fiye da mutane 300 da su ka warke sarai. Sai dai cutar ta samu ganin bayan mutane kusan 50 zuwa yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel