Faduwar farashin danyen mai alheri ne ga Najeriya - Atiku

Faduwar farashin danyen mai alheri ne ga Najeriya - Atiku

- Farashin danyen mai na ci gaba da faduwa a kasuwar duniya saboda annobar cutar korona

- Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ce karyewar farashin alheri ne ga kasar nan a fakaice

- Ya ce a yanzu Najeriya ta samu damar da za ta daina dogaro a kan albarkatun man fetur

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya ce karyewar da farashin danyen mai ya yi a kasuwar duniya alheri ne ga kasar Najeriya a fakaice.

Atiku ya ce kamata ya yi kasar Najeriya ta ribaci halin da kasuwar man fetur ta shiga ciki a matsayin wata dama ta yaye kanta daga dogaro a kan albarkatun man fetur wajen samun kudaden shiga.

Wazirin na Adamawa ya ce kamata ya yi faduwar farashin danyen mai a duniya ya kasance wani abun alfahari ga gwamnatin Najeriya da a yanzu za ta yiwa kanta karatun ta nutsu.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, babu shakka kifewar kwanan nan ta farashin mai ya haifar da babbar asara ga 'yan kasuwa da kasashen da ke hako mai a duniya.

Duk da cewa farashin danyen mai na Najeriya bai fada cikin bala'i ba tamkar na sauran kasashe masu arzikin man fetur, amma har yanzu akwai rashin tabbas a kasuwar sa.

A halin yanzu ana sayar da nau'in danyen mai na Najeriya wato Brent Crude wanda wasu ke kira Sweet Crude a kan $25.14 duk ganga guda, sabanin $45 zuwa $50 kafin barkewar annobar cutar COVID-19.

Masana man fetur na ganin cewa nau'in danyen mai na Najeriya ya fi na dukkanin sauran kasashe masu hako mai nagarta da inganci saboda karancin sunadarin Sulfur da ya ke da shi.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasara ranar Alhamis ya ce, wannan nagarta ba za ta tsinana komai ba duba da hadarin da ke tunkaro kasuwar man baya ga bala'in da ya afka mata a yanzu.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya; Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya; Atiku Abubakar
Source: Twitter

Atiku wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, ya gargadi Najeriya da ta tashi ta farga wajen sauya tunaninta na dogaro da man fetur.

Tabbas annobar cutar korona ce ke da alhakin disashewar kasuwar man fetur a duniya, lamarin da ya kara dugunzuma hankalin kasashen duniya.

Annobar korona ita ce sanadiyar faduwar farashin man fetur a duniya sanadiyar yadda al'amuran gudanarwa a kowace kasa suka tsaya cik.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Hakika an rasa masu sayan man fetur saboda yadda masana'antu da kamfanoni suka daina aiki, yayin da rumbunan ajiyarsa suka cika makil kuma babu mabukatansa.

Masu lura da tattalin arziki sun tabbatar da bushewar kasuwar man fetur, kuma bukatarsa ta ragu yadda ba a tunani a yayin da duniya ta kasance kusan a kulle babu fita.

Ana iya tuna cewa a farkon watan Afrilu ne mambobin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, suka amince a kan rage yawan man fetur da kowace kasa za ta rika fitarwa kasuwa.

OPEC ta yanke wannan hukuncin ne domin farfado da darajar man fetur a kasuwannin duniya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan lamari zai haddasa tabarbarewa tattalin arzikin Najeriya a sanadiyar yadda faduwarsa ta sauya hasashen da kasar tayi a cikin kasafin kudinta na bana.

Gwamnatin Najeriya ta dogara da arzikin man fetur wajen samun kashi 90% na kudaden shigarta a hasashen da tayi cikin kasafin kudin bana.

Gwamnatin kasar tun a watan Dasumba na 2019 yayin shigar da kasafin kudinta na bana, ta kiyasta farashin man fetur a kan $57 a duk ganga.

Daga bisani bayan da annobar korona ta dagula al'amura, ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, ta sanar da rage fiye da Naira biliyan 320 daga kasafin kasar na bana.

Sabanin yadda majalisar ta amince a baya, a yanzu an kiyasta farashin man fetur a kan $30 na kowace ganga. Yanzu kuma da lamurra suka ci gaba da tabarbarewa dole ne kasar ta sake nazari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel