COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno

COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno

Ba kamar yadda aka bada dalilin mutuwar Shehun Bama na jihar Borno, Alhaji Kyari El-Kanemi ba, jaridar SaharaReporters ta gano cewa annobar COVID-19 ce ta kashe shi.

El-Kanemi ya rasu ne a ranar Litinin a garin Maiduguri kuma an birneshi ne a ranar Talata a farfajiyar fadarsa da ke garin Bama.

COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno
Hoton marigayi Shehun Bama, Alhaji Kyari El-Kanemi a yayin da yake lafiya kalau. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

Amma kuma gwamnatin jihar ta ki sanar da ciwon da ya yi ajalin basaraken.

Majiya daga fadar ta tabbatar wa da jaridar SaharaReporters cewa a ranar Alhamis ne basaraken da dan majalisa mai wakiltar mazabar Nganzai, Wakil Bukar suka rasu sakamakon cutar Covid-19.

Sun rasu ne jim kadan bayan an kwantar da su a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri.

COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno
Masana kiwon lafiya da suka iso da gawar Shehun Bama. Hoton daga SaharaReporters
Asali: Twitter

"Jama'ar garin Bama sun fusata da gwamnatin jihar wacce ta kasa bayyana dalilin mutuwar Shehu don wadanda suka yi mu'amala da shi su killace kansu.

"Ya karba baki masu tarin yawa bayan mutuwar Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa wanda ya kasance dan asalin garin Bama kuma shakikin abokinsa.

"A halin yanzu, an killace sama da mutane 100 a fadar Shehun amma kuma an bar bakin da suka ziyarcesa ba tare da an sanar dasu abinda ya kasheshi ba.

"Hakazalika, an killace wadanda suka yi masa wankan gawa.

KU KARANTA: Mace-macen Kano: Ba zan ci amanar Kanawa ba - Buhari

"Saboda haka ne babu wani jami'in gwamnati da ya halarci jana'izarsa," cewar majiyar.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, Gwamna Babagana Zulum da mataimakinsa, Umar Kadafur basu halarci jana'izar ba. Hakazalika sauran manyan sarakunan biyu.

"A lokacin da aka kawo gawarsa daga Maiduguri, ta iso ne tare da jami'an tsaro masu tarin yawa kuma an hana jama'a halartar jana'izarsa," majiyar ta kara da cewa.

COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno
Yadda aka hana jama'a kusantar kabarin Shehun Bama yayin da ake birneshi. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

"A yayin da ake birne shi, an yi amfani da ababen hawa wajen toshe hanyar wucewa don hana jama'a isa wurin," ya kara da cewa.

Idan za mu tuna, jaridar SaharaReporters ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Mohammed Goni wanda ya rasu a ranar Laraba, ya fara nuna wasu alamu na cutar COVID-19.

An gano cewa Goni ya samu cutar ne a yayin da ya je jana'izar mahaifin tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff.

Jama'a da yawa sun halarci jana'izar wadanda kuma basu saka takunkumin fuskan ba don kiyaye dokokin NCDC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel