Zamfara: Ana neman wani mai dauke da cutar COVID-19 ruwa a jallo

Zamfara: Ana neman wani mai dauke da cutar COVID-19 ruwa a jallo

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana neman wani Jamilu Shinkafi ruwa a jallo saboda tsere wa da ya yi bayan an masa gwaji an kuma gano yana dauke da kwayar cutar coronavirus.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Yahaya Kanoma ya shaidawa The Punch cewa Shinkafi ya tsere bayan an tabbatar yana dauke da cutar da coronavirus.

Ya ce an tsananta bincike domin gano inda ya shiga ya boye.

"Muna nan muna neman sa. A jiya yana Abuja yau kuma ya tafi Kaduna. Tabbas za mu kamo shi.

"Mun sanar da Maaikatar Lafiya wannan abin bakin cikin kuma da ikon Alla za mu gano inda ya ke mu kama shi," in ji shi.

Zamfara: Ana neman wani mai dauke da cutar COVID-19 ruwa a jallo
Zamfara: Ana neman wani mai dauke da cutar COVID-19 ruwa a jallo
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ana takaddama kan kama matashin da ya yi wa Annabi batanci

Kanoma ya ce gwamnatin jihar ta Zamfara ta bayar da umurnin yi wa gidan Jamilu feshin maganin kashe kwayoyin cuta da ma unguwan su baki daya.

Ya yi kira ga alummar unguwar da suka yi cudanya da Jamilu a baya bayan nan su tafi cibiyar yin gwaji domin a gwada su nan take.

A wani rahoton kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta raba wa jihohi 24 a kasar Kudi Naira Biliyan 43,416 a matsayin tallafi cikin kudin da Bankin Duniya ta bawa jihohi bisa laakari da jajircewa da suke yi wurin yaki da cutar.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed cikin sanarwar da ta fitar ya nuna cewa jihohin da suka amfana da tallafin sun hada da Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe.

Sauran sune Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Ogun, Oyo, Osun, Sokoto, Taraba da Yobe states.

A cewar sanarwar mai dauke da saka hannun Direktan yada labarai na maaikatar, Hassan Dodo, kawo yanzu an raba wa jihohi 24 jumullar kudi N43,416,000,000.00 wanda ya yi dai dai da Dalla Miliyan 120.6.

Jihar Kaduna ce kan gaba wurin cika kaidojin samun tallafin hakan ya sa ta fi samun kaso mafi tsoka na N3,960,000,000.00.

Jihohin Katsina da Benue ne suka samu kaso mafi karanci na N540,000,000.00 kowannen su.

Ministan ya yi bayanin cewa an yi rabon tallafin ne bisa laakari da kiyaye kaidojin samun tallafin da ake gudanarwa a duk shekara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel