Jihar Kano ta sha gaban Abuja a yawan ma su dauke da kwayar cutar covid-19
A cikin kasa da sati uku da bullar annobar covid-19 a Kano, yanzu haka jihar ta zama ta biyu a yawan ma su dauke da kwayar cutar a Najeriya.
Ana ware adadin mutanen da suka mutu ko aka sallama idan ana duba yawan masu dauke da kwayar cutar covid-19 a jiha ko kasa.
A cikin sanarwar da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta fitar ranar Alhamis, jihar Kano ta koma mataki na biyu a yawan ma su dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.
Akwai jimillar mutane 136 da aka tabbatar sun kamu da cutar covid-19 a jihar Kano, yayin da jihar Legas, wacce ke mataki na daya, keda jimillar mutane 718 da aka tabbatar kwayar cutar ta harba.
Babban birnin tarayya, Abuja, da a baya ke bin jihar Legas, ya koma mataki na uku da adadin mutane 135 da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar covid-19.
An fara samun labarin bullar annobar covid-19 a Kano a ranar 11 ga watan Afrilu. Wani tsohon jakadan Najeriya ne ya fara kai kwayar cutar Kano daga Abuja.
Masana da kwararru sun bayyana damuwarsu a kan bullar annobar covid-19 a Kano saboda yawan jama'ar da jihar keda su.
Rahotanni na yawan kawo labarin mutuwar mutane a Kano. Amma, gwamnatin jihar Kano ta ce wasu cututtuka daban ne ke kashe mutane, ba annobar covid-19 ba.

Asali: Twitter
NCDC ta bayyana cewa ya zuwa yanzu ta gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a kan mutane 13,689.
Daga cikin jimmilar mutanen da aka gwada, an samu mutum 1,728 da ke dauke da kwayar cutar.
An samu bullar annobar covid-19 a kusan dukkan jihohin Najeriya 36, idan aka cire jihohin Kogi da Kuros Riba, wadanda har yanzu ba a samu rahoton bullar annobar ba.
NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:50 na daren ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu, akwai jimillar mutane 1728 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.
DUBA WANNAN: A karshe, sojojin Najeriya sun kwace kauyen Bula Shatane, 'yan Boko Haram sun mika wuya
An sallami mutane 307 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 51.
Alkaluman wadanda annobar covid-19 ta harba da NCDC ke fitarwa a 'yan kwanakin baya bayan nan na nuni da cewa annobar tana kara karfi a arewacin Najeriya.
Kwamishinan lafiya a jihar Borno, Dakta Salihu Kwayabura, ya ce alamu sun nuna cewa kwayar cutar covid-19 ta yadu a tsakanin jama'a. Ya ce akwai bukatar bullo da sabbin dabarun binciko wadanda annobar ta harba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng