Ana zargin Boss, Garba Shehu da wasu manya da sabawa doka wajen bizne Kyari

Ana zargin Boss, Garba Shehu da wasu manya da sabawa doka wajen bizne Kyari

Wani lauya mai suna Tope Akinyode ya shigar da karar manyan da su ka halarci jana’izar Abba Kyari a wani kotun majistare da ke unguwar Wuse a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan lauya ya zargi jami’an gwamnatin tarayya da wasu na kusa da shugaba Muhammadu Buhari da sabawa dokar zaman gida da gwamnati ta sa saboda annobar COVID-19.

Wadanda Tope Akinyode ya kai kotu sun hada da sakataren gwamnatin tarayya watau Boss Mustapha da kuma mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Sauran wadanda ake kara a kotun sun hada da ministocin harkokin kasar waje da na sufurin jiragen sama; Geoffrey Onyema da Hadi Sirika, da kuma shugaban NIA, Ahmad Rufai.

Lauyan ya na zargin har da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Babagana Munguno da laifin sabawa dokar da gwamnati ta sa a wajen bizne tsohon hadimin na Aso Villa.

KU KARANTA: Mutanen da ake tsammanin za su dare kujerar da Kyari ya mutu a kai

A karar da wannan lauya ya shigar mai sakin layi tara, ya zargi hadiman shugaban kasa: Lawal Kazure, Musa Dauda, Yusuf Sabiu, da Bashir Ahmed da laifin kin bin dokar gwamnati.

Aliyu Sani, da minista Hajiya Sadiya Umar-Farouq su ne ragowar wanda lauyan ya ce sun halarci bizne Malam Abba Kyari. Tope Akinyode ya ce ya kalli jana’izar ne a wani gidan talabijin.

Daga baya sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya tabbatar da cewa an samu cinkoso, kuma an saba dokar tazara wajen bizne shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyar.

A karar, lauyan ya gabatar da hotuna da bidiyoyi domin ya gamsar da shari’a. Lauyan ya ce ya shigar da wannan kara a kotu ne domin ayi adalci, jaridar Punch ta bada wannan rahoto.

Dama can wannan lauya ya yi alkawarin zai kai mukarraban gwamnatin Najeriyar kara a kotu da zargin sabawa dokar da Muhammadu Buhari ya sa da nufin rage yaduwar Coronavirus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel