Coronavirus: An samu wanda ya fara kamuwa da cutar COVID-19 a Yobe

Coronavirus: An samu wanda ya fara kamuwa da cutar COVID-19 a Yobe

Bayan tsawon lokaci an samu bullar cutar COVID-19 a jihar Yobe a makon nan. Kafin yanzu jihar ta na cikin inda ba a taba samun wanda ya ke dauke da wannan muguwar cuta ba.

Rahotannin da aka samu daga hukumar NCDC sun bayyana cewa gwaji ya nuna an gano mutumin farko da ya kamu da cutar COVID-19 ne a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu.

A jiya ranar Laraba da daddare, NCDC mai takaita yaduwar cututtuka a Najeriya ta tabbatar da cewa jihar Yobe ta na cikin jihohin da wannan cuta ta Coronavirus ta bulla a Najeriya.

Sakamakon gwajin da aka yi ya nuna cewa an gano sababbin mutane 196 da ke dauke da kwayar cutar COVID-19. Legas da Kano ne kan gaba, jihar Yobe ta samu mutum guda ne rak.

A daren jiya wadanda aka samu da cutar a jihar Legas sun haura mutum 20. Haka zalika a Kano an samu mutane 18. A jihar Gombe inda abin ya rikide, an samu mutane 17 da cutar.

A jihar Kaduna an gano karin mutane 16 da ke dauke da cutar wanda ake zargin mafi yawancinsu almajirai ne daga jihar Kano. Mutane 8 aka tabbatar su na dauke da cutar a Katsina.

KU KARANTA: Mutane da-dama sun warke da COVID-19 ba tare da sun nemi magani ba

Bayan rahoton da hukumar NCDC ta fitar a ranar Laraba, Yobe ta fita daga jerin jihohin da COVID-19 ba ta bulla ba. Yanzu jihohin biyu kadai su ka tsira daga wannan annoba.

Jihohin da ba a samu mai dauke da kwayar cutar COVID-19 a Najeriya ba su ne Kuros Riba da kuma jihar Kogi. Babu labarin mai dauke da wannan cuta a wadannan jihohi har yanzu.

Babu wani karin bayani game da yadda cutar ta shiga Yobe. Duk da haka dai Yobe, Ebonyi, Kebbi, Nasarawa, Imo, Bayelsa, Benuwai, da Filato su na cikin inda annobar ba ta yi kamari ba.

Mutane 1728 aka tabbatar da cewa sun kamu da COVID-19 a Najeriya. Daga ciki an yi nasarar sallamar fiye da 300 daga asibiti, inda cutar ta kashe mutane 51 a cikin watanni biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel