Ministan kwadago ya kaddamar da kwamitin da zai dauki ma’aikatan musamman

Ministan kwadago ya kaddamar da kwamitin da zai dauki ma’aikatan musamman

A farkon watan Afrilun nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki mutane 774, 000 haya domin su yi wasu ayyuka na musamman a lokacin annobar cutar COVID-19.

A cikin makon nan gwamnatin tarayya ta motsa domin ganin fara tsarin yadda za a yi wannan aiki. A ranar 29 ga watan Afrilu, aka kaddamar da kwamitin da ke da alhakin wannan aiki.

Karamin ministan kwadagon Najeriya, Festus Keyamo, shi ne ya rantsar da wannan kwamiti a karkashin shugaban hukumar nan ta NDE mai alhakin samar da ayyukan yi da koya sana’o’i.

Festus Keyamo ya kara jaddada aniyar gwamnatin Buhari na daukar mutane 774, 000 da za su yi aiki a lokacin wannan annoba. Najeriya ta na cikin kasashen da ake fama da cutar COVID-19.

Wadanda za a dauka haya za su yi wannan aiki ne na tsawon watanni uku. Za a zakuko mutum 1, 000 daga kowace karamar hukuma. Ana kuma da kananan hukumomi 774 a jihohin Najeriya.

KU KARANTA: Mutanen Afrika za su yi fama da karancin abinci a dalilin Coronavirus

Darekta Janar na NDE watau Dr. Nasiru Ladan shi ne shugaban wannan kwamiti da ministan ya rantsar. Kwamitin ya na da wakilci daga ma’aikatu takwas domin gudanar da wannan aiki.

An zakulo wakilan kwamitin ne daga cikin ma’aikatar tattalin arziki da kasafin kudi, ma’aikatar muhalli, ma’aikatar sufuri, ma’aikatar kiwon lafiya, sai ma’aikatar noma da raya karkara.

Haka zalika kwamitin zai yi aiki da ma’aikatar ruwa, ma’aikatar gidaje da ayyuka, da kuma ita kanta ma’aikatar kwadago da samar da aikin wanda a karkashinta ne ake daura kwamitin.

Ma’aikatar kwadagon ta bayyana cewa an yi wannan zama ne a jiya inda aka fitar da hotunan taron farko na kwamitin a shafin Tuwita. Kawo yanzu ba a san matsayar da aka cinma ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel