Ba za mu iya wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar tallafin COVID-19 ba – Ministar Buhari

Ba za mu iya wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar tallafin COVID-19 ba – Ministar Buhari

- Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar shirin bayar da tallafi na coronavirus ba

- Ministar walwala da jin dadin jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta ce ya saba ma tsarin aiki wallafa sunayen mutanen da suka amfana daga shirin domin hakan zai shafi martabar su

- Ta kuma jadadda cewar sun yi rabon kayayyakin yadda ya kamata inda a yanzu haka na jahar Kano ke a kan hanya

Ministar walwala da jin dadin jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta ce ya saba ma tsarin aiki wallafa sunayen mutanen da suka amfana daga shirin tallafi na gwamnati.

Da take magana a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu, a lokacin zaman kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, ministar ta ce ya saba ma “martabar dan Adam” tallafa wa mutum da kuma fallasa shi a bainar jama’a.

Ba za mu iya wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar tallafin COVID-19 ba – Ministar Buhari

Ba za mu iya wallafa sunayen wadanda suka ci moriyar tallafin COVID-19 ba – Ministar Buhari
Source: Facebook

Ta bayyana cewa gwamnati ta yi rikodin wadanda suka ci moriyar shirin bayar da tallafin kudi na hannu da hannu, da kuma wadanda suka amfana daga shirin rage radadin COVID-19 a jihohi, kananan hukumomi da garuruwa.

“An bamu kayan hatsi tan 70,000. Zuwa yanzu, mun yi nasarar kai tan 9,320 na hatsi zuwa wadannan yankuna uku da abun ya shafa. Kimanin tireloli 334 kenan, yayin da na Kano ke kan gudana. Tireloli 50 sun kusa isa Kano,” in ji ta.

KU KARANTA KUMA: An yi wa Gwamna Matawalle wankin babban bargo kan siya wa kwamishinoni manyan motocin alfarma

Ana dai ta sukar tsarin rabon kayan tallafin a fadin kasar.

Wata kungiyar jama’a mai suna HEDA, ta zargi gwamnati a dukkan matakai da gaza wa yan Najeriya.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta raba wa jihohi 24 a kasar Kudi Naira Biliyan 43,416 a matsayin tallafi cikin kudin da Bankin Duniya ta bawa jihohi bisa laakari da jajircewa da suke yi wurin yaki da cutar.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed cikin sanarwar da ta fitar ya nuna cewa jihohin da suka amfana da tallafin sun hada da Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe.

Sauran sune Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Ogun, Oyo, Osun, Sokoto, Taraba da Yobe states.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel