Boko Haram: Bana bukatar dakarun Najeriya su sassautawa 'yan ta'adda - Buhari

Boko Haram: Bana bukatar dakarun Najeriya su sassautawa 'yan ta'adda - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dakarun sojin kasar nan da su ci gaba da ruwan wutar da suke yi a yankin tafkin Chadi da kuma yankin Arewa maso gabas din kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya yi wannan jawabin a fadar shugaban da ke Abuja, yayin da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ziyarcesa, ya ce akwai bukatar jami'an tsaron kasar nan su ci gaba da kiyaye matsayarsu don kawo karshen Boko Haram.

Shugaban kasar ya jinjinawa kokarin dakarun sojin kasar nan a kan kokari da kuma nasarorin da suke samu wajen yakar 'yan ta'addan.

Ya kara da jan kunnen dakarun da kada su yi saken da zai sa 'yan ta'addan su samu mafaka a dukkan kasar nan. Hakan zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaban da ake bukata.

Buhari ya ce akwai bukatar fatattakar ta'addanci don tabbatar da noma tare da dawowar sauran al'amuran ci gaban kasa a yankin.

Ya kara jaddada cewa kiwon lafiya da zaman lafiyar kasar nan ya danganta da kokarin kasar wajen ciyar da kanta. Don haka, noma da kiwo ne kashin bayan ci gaban al'umma.

Boko Haram: Bana bukatar dakarun Najeriya su sassautawa 'yan ta'adda - Buhari
Hoton Shugaba Buhari tare da gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a fadar shugaban kasa. Hoto daga jaridar Herald
Asali: Twitter

KU KARANTA: Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

Buhari, wanda ya yi kira ga gwamnan jihar Yoben da ya ci gaba da goyon bayan sojojin, ya ce rahotannin sirri a tsakanin hukumomi da farar hula za su matukar taimakawa.

Gwamna Buni, wanda ya bayyanawa shugaban kasar halin tsaro da jiharsa ke ciki, ya mika godiya ga gwamnatin tarayyar a kan irin matakin da take dauka wanda ke tada hankulan 'yan ta'addan.

Ya ce an samu nasarori masu tarin yawa daga rundunar sojin tun bayan kokarin da dakarun kasar Chadi suka yi.

Buni ya sanar da shugaban kasar cewa, matukar dakarun sojin suka ci gaba da kokarin da suke yi, Boko Haram ta kusa zama tarihi.

Kamar yadda aka sani, a halin yanzu dakarun sojin Najeriya sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sakewa a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel