Kano: Mutum 45 sun shiga hannun hukuma bayan karya doka

Kano: Mutum 45 sun shiga hannun hukuma bayan karya doka

- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da damko mutum 45 da aka kama da laifin take dokar jihar

- Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana, 15 daga cikinsu malamai ne da suka ja sallar Juma'a a jam'i

- Shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 ta jihar, ya tabbatar da cewa an yi nasarar damko wani mutum da ya gudu bayan an tabbatar da yana dauke da cutar Korona

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta damke mutum 45 a kan zarginsu da ake da karya dokar hana zirga-zirga a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Habu Sani, ya bayyana hakan yayin bada bayanin inda aka tsaya wajen tabbatar da dokar hana zirga-zirga a jihar.

Ya ce 15 daga cikin wadanda ake zargin duk malamai ne. An kama su ne saboda jan jam'in sallar Juma'a da suka yi wanda ya yi karantsaye ga dokar jihar.

A halin yanzu dai an yanke musu hukunci, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan, wanda shine shugaban kwamitin jami'an tsaro a kan yakar COVID-19, ya ce mutum 30 ne aka sake kamawa a kan wannan laifin kuma an yanke musu hukunci.

Kano: Mutum 45 sun shiga hannun hukuma bayan karya doka

Kano: Mutum 45 sun shiga hannun hukuma bayan karya doka
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

"Muna kokarin wayar da kan jama'a a cikin yankunansu don su fahimci illar abinda suke aikatawa," ya kara da cewa.

A halin yanzu, an damko daya daga cikin mutum uku da aka gano suna dauke da cutar Korona a jihar.

Bayan an tabbatar da yana dauke da cutar, ya tsere sannan ya boye amma an kama shi.

Daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa kuma shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jihar, Farfesa Isah Abubakar ya tabbatar da kamen a ranar Laraba.

Ya ce an kwashe majinyatan inda aka kaisu daya daga cikin cibiyar killacewa ta jihar Kano.

A halin yanzu ana ci gaba da bibiya tare da binciko wadanda suka gudu bayan sun tabbatar da cewa suna dauke da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel