Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan masu yunkurin siyasantar da mace-macen da ake yi a jihar Kano. Ta ce babu lokacin bata wa don cimma wasu burikan siyasa a halin yanzu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, akwai yuwuwar fadar shugaban kasa ta yi martani a kan wasikar da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya rubuta.

A cikin wasikar, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya mayar da hankali a kan al'amuran jihar Kano.

Ya zargi shugaban kasan da nuna halin ko in kula da kuma rashin tsari a yayin yakar cutar Covid-19 a jihar.

Wasikar Kwankwaso ta fita ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi hira da BBC. Ya zargi cewa an ware jihar yayin yakar annobar COVID-19 a matakin tarayya.

A yayin martani ga wasikar, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya shawarci 'yan kasa da su shirya rungumar sakamakon binciken da ake yi na mace-macen jihar Kano.

Ya ce a shirya aiki da kwararru don tunkarar babban makiyinmu a halin yanzu.

Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi
Budaddiyar wasikar Kwankwaso: Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru

"Makonni kadan kenan da Najeriya ta fara wannan yakin da makiyin da ba a gani wanda ya gallabi kusan kowacce kasa.

"A cikin kwanakin nan ne WHO ta bayyana cewa yanzu nahiyar Afrika ta fara yakin nan.

"Akwai abubuwa masu yawa da bamu sani ba game da cutar. Abinda kadai muka sani shine yadda cutar ke yaduwa a duniya a kowacce rana.

"Mun san cewa akwai karancin kayayyakin kariya a duk fadin duniya, rashin kayan gwaji da sauran abubuwan bukata don yakar cutar," yace.

Kamar yadda takardar ta bayyana, sanannen abu ne idan aka ce akwai wuraren da cutar ta fi kamari a Najeriya.

"Wannan ba lokacin bata wa bane wajen cimma manufofin siyasa ba. Koda ka kasance tsohon dan siyasa a matakin jiha ko na tarayya, wannan ba lokacin surutu bane.

"Dukkanmu neman mafita muke yi don tseratar da rayuka da lafiyar 'yan kasa," Garba Shehu yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel