COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana wasu sharudda da yace dole a cike su kafin ya sassauta dokar hana zirga-zirga ta jihar Kaduna wacce aka kara wata daya a kai.

A tattaunawar kai tsaye da aka yi da gwamnan a gidajen rediyo a daren Talata, gwamnan ya ce in har jihar ta iya gwajin mutum 1,000 a rana daya za a sassauta dokar, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, matukar aka iya dakile yaduwar cutar ta hanyar masu shigowa daga wasu jihohi, zai duba yuwuwar sassautawa.

Ya ce, "Idan muka iya gwajin jama'a masu yawa kuma cutar bata barke ba, wannan karin kwanaki 30 din zai koma kwanaki 10 ko 14 ko kuma bakwai kacal."

Ya kara da bayyana cewa, "Muna fatan matukar dakin gwajin cutar na uku wanda za a yi a asibitin Yusuf Dantsoho ya kammala a cikin makon nan, za mu iya sassauta dokar."

COVID-19: El-Rufai ya bada sharuddan sassauta doka a jihar Kaduna

COVID-19: El-Rufai ya bada sharuddan sassauta doka a jihar Kaduna
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Buhari ya nada mambobin hukumar FCC guda 38

Gwamnan ya ce tuni dakunan gwaji biyu da ke jihar suka kammala kuma NCDC ta amince dasu. Tuni za a fara gwajin mutum 1,000 a kowacce rana a jihar.

Ya kara da cewa, "Muna tabbatar da cewa babu jama'ar da ke shigowa daga sauran jihohi, za mu sassauta dokar ko kuma dakatar da ita don jama'a su ci gaba da hada-hadarsu.

"A yayin da muke wannan halin, za mu tabbatar da cewa mun dakile duk wata shige da fice daga sauran jihohi."

Gwamnan ya kara da cewa, suna sane da shirin wasu 'yan kasuwa da ke kokarin tada zanga-zangar lumana bayan gwamnati ta sanar da cewa za ta rufe kasuwanni tare da kafa na wucin-gadi.

Ya kara da jan kunne, "Muna jiran duk wanda zai fito zanga-zanga. Mun umarci sojoji da 'yan sanda da su fito. Duk wanda ya yi tunanin zai iya tada zaune-tsaye a jihar a wannan lokacin, zai fuskanci fushin hukuma.

"Wadannan kasuwannin duk mallakin gwamnati ne ba jama'ar gari ba. Gwamnati ce ta gina kuma duk wanda ya ke tunanin ya mallaki shago, ya fito.

"Kowacce irin takarda ka mallaka, ina da tabbacin babu ta filin, don na gwamnati ne. Don haka duk wanda zai tada hankula, ya san cewa muna da dokokin natsar dashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel