Alhamdulillah: Saudiyya za ta bude masallatan Makkah da Madina

Alhamdulillah: Saudiyya za ta bude masallatan Makkah da Madina

Babban limamin Masallatan biyu masu daraja a addinin Musulunci na Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Al-Sudai ya bayyana cewa nan bada jimawa za’a bude masallatan biyu.

Sudais ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo a ranar Talata, inda ya baiwa jama’a Musulmai tabbacin cewa za’a cigaba da bauta a masallatan nan bada jimawa ba.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal

“Ranakun bakin ciki zasu kare, kuma al’ummar Musulmai za su cigaba da bauta a Masallatai biyu masu daraja, zasu cigaba da dawafi, sa’ayi tsakanin safa da marwa da kuma sallah a cikin Rawdah domin su gaishe da Annabin Allah.

“Komai zai dawo kamar yadda aka saba da ikon Allah, saboda gwamnati na kokarin tabbatar da ingantaccen yanayin kiwon lafiya.” Inji shi.

Alhamdulillah: Saudiyya za ta bude masallatan Makkah da Madina
Alhamdulillah: Saudiyya za ta bude masallatan Makkah da Madina
Asali: Facebook

Don haka Sheikh Sudais ya yi kira ga Musulmai da kada su kosa a janye dokar hana shige da ficen da gwamnati ta sanya domin dakile yaduwar annobar Coronavirus.

Haka zalika babban limamin ya bayyana cewa gwamnatin Saudiyya za ta sanya na’urar daukan hoto masu lura da dumin jikin dan Adam don gane masu dauke da cutar COVID19.

“Mun gode ma Allah, a yau mun kaddamar da na’urar daukan hoto mai lura da dumin jikin dan Adam wanda zai iya gwada dumin jikin mutane 23 a lokaci daya daga kofar shiga cikin masallacin, idan har mutum na dauke da cutar, na’urar za ta nuna shi.” Inji shi.

A hannu guda, fiye da mutane 700 ne suka mutu bayan sun kwankwadi barasa a matsayin maganin annobar Coronavirus a kasar Iran, domin a tunaninsu giya tana maganin cutar.

Aljazeera ta ruwaito hukumar yaki da Coronavirus a kasar Iran ce ta bayyana haka, inda tace mutane 728 ne suka mutu daga watan 20 ga watan Feburairu zuwa 17 ga watan Afrilu.

Gwamnatin Iran ta ce an samu karuwar mace mace daga shan barasa ninki 10 a shekarar daya data gabata, inda a shekarar 2019 aka samu mutane 66 da suka mutu sakamakon shan giya.

Kakaakin ma’aikatar kiwon lafiya na Iran, Kianoush Jahanpour ya ce mutane 5,011 ne suka sha sinadarin Methanol dake cikin giya, mutane 90 sun rasa idanunsu a dalilin haka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel