Kano: Bincike ya alakanta cutar Korona da mace-mace a jihar

Kano: Bincike ya alakanta cutar Korona da mace-mace a jihar

A mace-macen da aka fuskanta a jihar Kano, jinsin maza ne suka kwashe kashi 91 cikin dari, bincike ya bayyana.

Kamar yadda binciken da jaridar The Cable ta gani ya bayyana, kashi 41.3 daga cikin mamatan sun mutu ne bayan zazzafan zazzabi, alama ta cutar coronavirus.

A cikin makonnin da suka gabata, an dinga samun mace-mace a jihar Kano ta manyan sanannun jama'a.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan a ranar Lahadi amma sai ta dangana hakan da zazzabin cizon sauro ba annobar Coronavirus ba.

An gano cewa, yaduwar kwayar cutar a dakin gwaji na jihar ne ya munanta lamarin.

Hakan kuwa yasa aka dinga hasashen cewa annobar ce ta lashe rayuka da dama.

Muhammad Garba, kwamishinan lafiya na jihar Kano, ya bayyana cewa sun tuntubi iyalan mamatan kuma sun tattara bayanai daga ciwon da ya kashe mutanen. Da shi za a yi amfani wajen bankado matsalar.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta aminta da tattaunawa da iyalan mamatan don gano tushen matsalar mutuwar da ba a san tushenta ba, amma akwai ka'idojin kiyayewa.

Tun bayan mace-macen, Yusuf Yau Gambo, malami a fannin lissafi na jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano ne ya fara binciken. Ya bada dalilin da yake tunanin ya jawo hakan a babban birnin Kano.

Gambo, wanda ya ce rahoton ya jawo hankalin kwamitin yakar cutar coronavirus na jihar Kano, ya ce an yi shi ne don fahimta tare da kawo karshen bayanan bogin da ke yawo.

An yi binciken ne a gidaje 260 da ke kananan hukumomi 17 na jihar. A ciki kuwa sune suka kunshi iyalan mamatan ko kuma wadanda suka rasa a kalla mutum biyar a yankin.

Kashi 67 sun bayyana cewa an fara mace-macen ne a ranar 13 ga watan Afirilu kuma ya ci gaba har zuwa ranar da aka kammala binciken.

Rahoton ya nuna cewa, da yawan mace-macen sun auku ne a tsakiyar birnin Kano da kananan hukumomin Gwale da Dala.

Rahoto ya nuna cewa zazzabi ne ya kashe mamatan inda kashi 22 kacal ne suka kai ga asibitin kafin mutuwarsu.

Kano: Bincike ya alakanta cutar Korona da mace-mace a jihar
Yawan jama'ar da suka rasu cikin kwanakin nan a kananan hukumomin jihar Kano
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya

Kashi daya bisa ukun wadanda suka rasun sun dauka kasa da kwanaki biyar ne suna zazzabin.

Wani likita mai suna Auwal Abubakar mai aiki da cibiyar taimakon gaggawa ta jihar Bauchi ya alakanta sakamakon binciken da cutar coronavirus.

"Duk da akwai matukar wahala idan aka ce ga cutar da ta kashesu, amma ba zai yuwu a cire annobar COVID-19 daga hasashen ba.

"Akwai babbar alaka tsakanin alamun cutar coronavirus a matakin farko da kuma shekarun wadanda ta kama har ta kashe." Abubakar yace.

Kashi daya na mace-macen ne aka samu yara yayin da kashi 50 ya kunshi manya masu shekaru sama da 60.

Gambo ya ce, "Wannan rahoton zai bai wa hukumomin alkiblar daukar mataki. Ana shawartar jama'a da su kwantar da hankulansu har zuwa kammalawar binciken."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng