COVID-19: Mahaifi ya hana dansa shiga gida bayan ya dawo daga jihar Legas (Bidiyo)

COVID-19: Mahaifi ya hana dansa shiga gida bayan ya dawo daga jihar Legas (Bidiyo)

Wani mutum mai suna Femi Adeoye ya hana dansa wanda ya dawo daga tafiya shiga gidansa da ke Ekiti ba tare da an tabbatar da cewa baya dauke da cutar COVID-19 ba.

Adeoye ya ce dole ne a killace dansa na kwanaki 14 kamar yadda hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta gindaya don hana yaduwar cutar.

A halin yanzu, kwamitin yaki da cutar Covid-19 ta jihar ta jinjinawa Adeoye wannan kokarinsa na yakar annobar, jaridar Leadership ta wallafa.

A yayin da gwamnati ke martani a kan bidiyon Adeoye, ta ce "Adeoye ya nuna tsananin rashin son kansa wanda ta hakan ne ya tabbata a matsayin mai kishin al'ummarsa."

Takardar ta fito ne daga gwamnatin jihar wacce kwamishinan yada labarai, Muyiwa Olumilua yasa hannu.

Ta kara da cewa, "Muna son sanar da jama'a cewa an dauka bidiyon ne a kwanaki hudu da suka gabata. Wani jami'in tsaro ne da ke Fajuyi Pavilion ne ya dauka a yayin da yake aikin tabbatar da dokar hana walwala a jihar.

"An dakatar da jami'in tsaron da ya nadi bidiyon don an kama shi da laifin yin aikin da ba a saka shi ba."

KU KARANTA: COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

Kamar yadda takardar ta bayyana, an dauka samfurin jinin dan don tabbatar da cewa akwai cutar a jikinsa ko babu.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a jiya ya ce jihar na fuskantar babban kalubale sakamakon yadda annobar Covid-19 ke yaduwa. Hakan kuwa na bukatar taimakon gaggawa.

Gwamna Ganduje wanda ya yi jawabi yayin karbar kwamitin yaki da cutar Korona na fadar shugaban kasa a gidan gwamnati, ya ce jihar na cikin wani hali a kan cutar.

Ya ce: "Muna fuskantar kalubale daga kowanne bangare kuma muna bukatar taimako, ballantana yanzu da muka gane cewa a cikin garin ne sakamakon mu'amala cutar ke yaduwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel