Annobar covid-19 ta sake hallaka mutane uku a Maiduguri

Annobar covid-19 ta sake hallaka mutane uku a Maiduguri

Gwamnatin Borno ta sanar da sake samun mutuwar mutane uku da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar.

Ya zuwa yanzu, jimillar mutanen da annobar COVID-19 ta hallaka a jihar Borno ya karu zuwa mutum 6.

Kwamishinan lafiya a jihar Borno, Dakta Salihu Kwayabura, ne ya sanar da hakan yayin taron da ya saba yi da manema labarai a kullum.

Kwayabura ya ce dukkan mutane ukun da suka mutu basu da alaka da juna, kuma basu da alaka da mutum na farko da cutar cornavirus ta hallaka a jihar Borno.

A cewar kwamishinan, wannan alama ce da ke nuna cewa kwayar cutar covid-19 ta yadu a tsakanin jama'a. Ya ce akwai bukatar bullo da dabarun binciko wadanda annobar ta harba.

Yanzu haka wata tawagar kwararru ta fara bin sahun wasu mutane 230 da aka gano cewa sun yi mu'amala da mutanen da cutar covid-19 ta hallaka, a cewar kwamishinan.

Annobar covid-19 ta sake hallaka mutane uku a Maiduguri

Annobar covid-19 ta sake hallaka mutane uku a Maiduguri
Source: Twitter

Kwamishinan ya rufe jawabinsa da yin kira ga mazauna jihar Borno a kan muhimmancin tsaftar jiki da muhalli, amfani da takunkumi, nesantar jama'a, da wanke hannu da sabulu wajen yaki da kwayar cutar covid-19.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda a Kaduna sun kama wani dan Musulmai da ya zagi annabi a 'facebook'

A daren ranar Laraba ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 195 ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta wallafa a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha, inda ta bayyana cewa kawai mutane 11 daga jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel