An gano wani sabon lahani da cutar Coronavirus ke yi wa jikin dan Adam

An gano wani sabon lahani da cutar Coronavirus ke yi wa jikin dan Adam

- Farfesa Akin Abayomi, kwamishinan lafiya na jahar Lagas ya bayyana wasu sabbin abubuwa da suka gano tattare da annobar COVID-19

- Abayomi ya ce cutar Coronavirus na shafar lafiyar koda da jinin dan Adam

- Ya yi kira ga masu cutar suga, hawan jini da yawan kitse a jiki da su yi taka-tsan-tsan domin halin da suke ciki ka iya haifar da kamuwa da mummunar cutar

Kwamishinan lafiya na jahar Lagas, Farfesa Akin Abayomi, ya ce cutar Coronavirus na shafar lafiyar koda da jinin dan Adam.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu a lokacin wani shirin Arise News.

An gano wani sabon lahani da cutar Coronavirus ke yi wa jikin dan Adam
An gano wani sabon lahani da cutar Coronavirus ke yi wa jikin dan Adam
Asali: UGC

Kwamishinan ya yi gargadin cewa masu kitse a jiki, da ciwon suga da hawan jini su yi hankali sosai, domin halin da suke ciki ka iya haifar da kamuwa da mummunar cutar.

“Akwai sabbin abubuwa da aka gano game da annobar COVID-19. Misali, ba wai cutar lumfashi bace kawai kai tsaye. Mun gano cewa yana shafar jini da koda.

“Wadanda abun zai fi shafa sune masu ciwon suga, hawan jini da matsalolin garkuwar jiki. Masu kitse a jiki ma na cikin hatsari. Idan ka fada cikin kowani rukuni, ya zama dole ku yi taka-tsan-tsan,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Shahararren jarumin fina-finan Indiya Irrfan Khan ya rasu

A wani labarin kuma, mun ji cewa an kara samun sabbin mutane 38 da suka kamu da cutar annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar Kano, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana.

NCDC ta bayyana haka ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter a daren Talata, inda tace jimillan masu dauke da cutar a Kano sun kai 115.

“An samu karin mutane 195 da suka kamu da cutar COVID19 a Najeriya kamar haka 80 – Lagos, 38 – Kano, 15 – Ogun, 15 – Bauchi, 11 – Borno, 10 – Gombe, 9 – Sokoto, 5 – Edo, 5 – Jigawa, 2 – Zamfara, 1 – Rivers, 1 – Enugu, 1 – Delta, 1 – FCT, 1 – Nasarawa.

“Zuwa karfe 11:50 na daren Talata 28 ga watan Afrilu, jimillan masu dauke da cutar a Najeriya sun kai 1532, mutane 255 sun warke yayin da mutane 44 suka rigamu gidan gaskiya.” Inji NCDC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel