Karuwar masu cutar covid-19: Gwamnatin Jigawa ta rufe kananan hukumomi 3

Karuwar masu cutar covid-19: Gwamnatin Jigawa ta rufe kananan hukumomi 3

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe wasu kananan hukumominta guda uku bayan samun bullar annobar covid-19.

A ranar Talata ne hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da cewa sabbin mutane 195 sun kamu da kwayar cutar covid-19. Biyar daga cikin mutanen sun fito ne daga jihar Jigawa.

Da yake sanar da rufe kananan hukumomin guda uku, gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, ya ce an samu karin mutane biyu da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a gidan gwamnatin Jigawa da ke Dutse, babban birnin jiha.

A cewar Badaru, an tabbatar da samun kwayar cutar covid-19 a jikin wani mutum mazaunin garin Gujungu a karamar hukumar Taura.

Dayan kuma da aka samu yana dauke da kwayar cutar, dan asalin karamar hukumar Birnin Kudu ne amma yana aiki a karamar hukumar Gumel, lamarin da yasa dokar kullen ta shafi kananan hukumomi uku.

Sakamakon gwaji ya nuna cewa mutum na farko da aka samu da kwayar cutar covid-19 a jihar Jigawa ya warke, amma duk da haka za a sake gudanar da gwaji a kansa domin tabbatar da cewa ya warke ras.

"Labari mai dadi shine mutane biyu da ke dauke da kwayar cutar covid-19 a Jigawa suna samun sauki.

Karuwar masu cutar covid-19: Gwamnatin Jigawa ta rufe kananan hukumomi 3
Gwamnan Jigawa; Badaru Abubakar
Asali: Twitter

"Yanzu haka sakamakon gwaji ya nuna cewa mutum na farko mai dauke da kwayar cutar da aka dawo da shi Jigawa daga Kano ya samu sauki.

"Za a sake gudanar da gwaji na biyu a kansa domin kore duk wani shakku kafin a sallame shi.

"A bangare daya kuma, sakamakon gwajin da aka aiko mana daga Abuja ya nuna cewa mutane biyu sun sake kamuwa da cutar a Jigawa.

DUBA WANNAN: An sake yin rashin babban malamin jami'a a Kano

"Daya daga cikinsu dan garin Gujungu ne a karamar hukumar Taura, na biyun kuma dan karamar hukumar BirninKudu da ke aiki a karamar hukumar Gumel.

"A saboda hakane gwamnati ta saka dokar rufe garin Gujungu, BirninKudu da Gumel daga ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.

"Yin hakan ya zama wajibi saboda zai bawa gwamnati damar bin diddigi da gudanar da gwaji a kan mutanen da ake zargin sun yi mu'amala da mutanen biyu," a cewar Badaru.

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da rufe karamar hukumar Kazaure bayan samun mutum daya da annobar cutar covid-19 ta harba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng