Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Fintiri rasuwa

Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Fintiri rasuwa

- Allah ya yi wa Hajiya Fatimah Umar Badami, mahaifiyar gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa rasuwa

- Hajiya Fatimah Badami ta rasu ne a yau Laraba bayan ta yi gajeriyar jinya a asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola

- Ta rasu ne ta bar Gwamna Ahmadu Fintiri da jikoki hudu, sai 'yan uwa da abokan arziki

Allah ya yi wa Hajiya Fatimah Umar Badami, mahaifiyar gwamnan jihar Adamawa rasuwa.

Mahaifiyar Gwamna Ahmadu Fintiri ta rasu ne tana da shekaru 68 a duniya.

Hajiya Fatimah Badami ta rasu ne a yau Laraba a asibitin tarayya da ke Yola bayan gajeriyar rashin lafiyar da ta yi, kamar yadda takarda daga gidan gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana.

Takardar ta fito ne daga daraktan yada labarai da sadarwa na gidan gwamnatin, Solomon Kumangar.

Ya ce mamaciyar ta bar Gwamna Fintiri ne da jikoki hudu sai sauran 'yan uwanta.

"Mutuwar ta ta bar babban gibi ba ga iyalanta kadai ba, har da dukkan jihar. Ginshiki ce a jihar kuma Musulma ta gari," takardar tace.

Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Fintiri rasuwa

Allah ya yi wa mahaifiyar Gwamna Fintiri rasuwa
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Gwajin da aka yi wa likitocin China 15 da suka zo Najeriya ya fito

Ta kara da cewa: "Mutuwar ta matukar girgiza gwamnan amma yana bukatar addu'arku don samun rahama tare da fatan juriyar rashinta."

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mahaifin Fintiri ya rasu ne a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Ya rasu ne yana da shekaru 82 a duniya.

A wani labari na daban, tawagar kwarrarun ma'aikatan Lafiya 15 da suka zo Najeriya daga China domin taimakawa kasar wurin yaki da COVID-19 duk ba su dauke da kwayar cutar a cewar Ministan Lafiya, Osagie Ehanire.

Mr Ehanire yayin jawabin da kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da COVID-19 a ranar Talata ya ce sakamakon gwajin da aka yi ya nuna dukkan yan kasar na China ba su dauke da kwayar cutar.

Wannan na zuwa ne bayan sun kwashe kwanaki 14 a killace domin tabbatar da cewa ba su kamu da cutar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel