Na sha wahala ta tsawon kwanaki 26 a ware - El- Rufa'i

Na sha wahala ta tsawon kwanaki 26 a ware - El- Rufa'i

A karon farkon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana irin halin ha'ula'i da ya tsinci kansa har na tsawon kwanaki 26 a ware yayin da ya ke jinyar cutar korona.

A ranar 28 ga watan Maris ne aka gano cewa gwamnan ya kamu da cutar korona kuma ya kasance mutum na farko da cutar ta harba a duk fadin jiharsa ta Kaduna.

Bayan shafe tsawon kwanaki 26 yana jinya a ware, an sallami gwamnan bayan da ya samu waraka a ranar 22 ga watan Afrilu, inda sakamakon gwaji ya tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cutar.

A wata hira da wasu zababbun gidajen rediyo na Kaduna da ya yi a ranar Talata da daddare, Malam Nasiru ya ce ya sha fama da matsanancin ciwon kai da kuma zazzabi a makon farko da ya yi a killace.

Malam El-Rufa'i ya bayyana cewa ba ya da tabbaci a kan lokaci ko kuma wurin da ya kamu da cutar, amma dai yana zaton ya kamu da ita ne a birnin Abuja inda ya halarci taruka daban-daban.

Gwamnan ya ke cewa: "Na sha wahala sosai. An ware ni na tsawon kwanaki 26 ba tare da sanya iyali na a idanu na ba, ba wanda na ke iya gani face masu duban lafiya ta."

Gwamnan Kaduna; Malam Nasiru El- Rufa'i

Gwamnan Kaduna; Malam Nasiru El- Rufa'i
Source: UGC

"Ban samu damar ganin iyalai na har na tsawon kwanaki 26 ina killace. Har ta wanda aka wakilta ya rika kawo min abinci a koda yaushe yana sanye da kayan kare kai daga kamuwa da cutar. Kuma a kullum ina kan shan magani sau daya ko sau biyu a rana."

Duk da cewa alamomin cutar na tari ko matsalolin numfashi ba su bayyana a gare shi ba, sai dai ya zayyana irin bakar wahalar da ya sha ta matsanancin ciwon kai da zazzabi wanda ko makiyinsa ba ya masa fatan hakan ta same shi.

KARANTA KUMA: Sakacin da kasar China ta yi ya haifar da yaduwar cutar korona a duniya - Trump

Gwamnan ya bayyana cewa duk da cewa babu ko mutum guda da ya kamu da cutar a cikin iyalinsa ko dangi, sai dai ya gogawa wani abokin aikinsa, daya daga cikin direbobinsa, hadimin gida da kuma wani amininsa.

"Bayan mako na farko, na samu sauki kuma na fara karatu da nazari a kan yanar gizo game da duk abin da ya shafi coronavirus, kuma kusan na zama ƙwararren masani. Daga nan na yi amfani da lokacina wajen yin addu'a da karantun Kur'ani."

Gwamnan ya bayyana yadda sai da ta kai lokacin da likitoci suka karbe masa wayoyinsa, wadda yana tunanin hakan hadin bakin matansa ne da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, domin a hana sa amsa waya.

Da ya ke magana dangane da gemun da ya tsayar a yanzu, gwamnan ya ce tuni mahaifiyarsa ta ba shi umarnin kawar da shi domin kuwa mahaifinsa bai tsayar da gemu ba haka kuma yayansa, saboda haka ba ta ga dalilin da shi zai tsayar ba.

A karshe gwamnan ya nemi al'ummar jihar Kaduna da su kara hakuri da irin matakan da gwamnatinsa ta dauka tare da bada tabbacin cewa tun da kuwa ya sha fama da cutar korona, ya zama tilas ya tabbatar da tsaron lafiyar dukkanin al'ummar jiharsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel