P & ID: Gwamnatin Tarayya ta na binciken asusun Shugaba Jonathan da Diezani

P & ID: Gwamnatin Tarayya ta na binciken asusun Shugaba Jonathan da Diezani

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci a ba ta bayanan kudin da ke shiga cikin asusun wasu tsofaffin shugabanni da jami’an kasar wanda su ka rike mukami a lokacin mulkin PDP.

Daga cikin wadanda ake tunanin gwamnati ta na son samun rahoto game da asusun bankinsu har da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience Dame Jonathan.

Sauran wadanda ake bincike a kansu sun hada da tsofaffin ministocin man fetur Diezani Alison-Madueke da marigayi Rilwanu Lukman. Lukman dai ya rasu tun tsakiyar shekarar 2014.

Bankunan da ake bibiya su ne: Citigroup, JPMorgan Chase da kuma Deutsche Bank AG. Gwamnatin tarayya ta na binciken wata kwangilar gas ne da kasar ta yi da kamfanin P & ID.

Hukumar EFCC ce ta ke gudanar da bincike domin ta gano wadanda ke da hannu a badakalar da aka tafka a wannan kwangila da P & ID da sunan za a kafa wani kamfanin gas a Najeriya.

Ko da dai babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’ar kasar, Abubakar Malami bai kira sunan Goodluck Jonathan karara ba, ana zargin tsohon shugaban kasar da kuma ministarsa.

KU KARANTA: Jonathan da Atiku sun yi wa Buhari ta'aziyyar rasuwar Abba Kyari

P & ID: Gwamnatin Tarayya ta na binciken asusun Shugaba Jonathan da Diezani
Ana binciken asusun Shugaba Jonathan da na kusa da shi a Amurka
Asali: UGC

Dr. Goodluck Jonathan ya yi maza ya wanke kansa daga zargi. Jonathan ya fitar da wani dogon jawabi ta bakin mai magana a madadinsa watau Ikechukwu Eze a jiya ranar Talata da dare.

“Hankalinmu ya zo kan wani labari daga ketare cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta rubutawa bankuna takardar samun bayani kan Goodluck Jonathan da mai dakinsa Patience Jonathan.”

Mista Eze ya ce: “Gwamnatin Najeriya ba ta tuntubi Jonathan ko matarsa kafin su aika wadannan takardu ba. Idan da ta tuntubesu, da mun ba su shawarar ka da su rubuta wannan takarda.”

“Domin ba za ka iya rubuta takarda akan abin da babu shi ba. Za mu tunawa jama’a cewa a 2014 Jonathan ya shaidawa ministocin da ya rantsar cewa bai da asusu ko kadarori a kasar waje.”

Ikechukwu Eze ya ce ya tabbata daga 2014 zuwa yanzu babu abin da ya canza game da Jonathan wajen mallakar kadarori ko ajiye kudi a banki a kasar Amurka kamar yadda aka san sa tuni.

“Jonathan ya na kira ga hukumomin Amurka su ba gwamnatin Najeriya hadin-kai a wannan bincike da su ke yi.” A jawabin Jonathan ya wanke kansa daga hannu a kwangilar P & ID.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel