Fayemi ya zaftare 50% na albashin masu rike da mukaman siyasa a Jihar Ekiti
Domin a samu kudin da gwamnati za ta yi aiki, mai girma gwamnan jihar Ekiti watau Dr. Kayode Fayemi ya bada umarni a rage albashin da ake biyan wadanda ya ba mukaman siyasa.
Gwamna Kayode Fayemi ya bukaci wannan umarni da ya bada ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba. Gwamnan ya ce ya dauki wannan mataki ne a sakamakon rugujewar tattalin arziki.
Tattalin arzikin Duniya ya shiga matsala a sanadiyyar annobar cutar COVID-19. Danyen mai wanda Najeriya ta dogara da shi ya rage kudi a kasuwa, sannan kuma ya kan yi kwantai.
Kayode Fayemi ya bada wannan sanarwa ne ta bakin kwamishinan yada labarai na jihar Ekiti, Muyiwa Olumilua wanda ya ce za a karkatar da kudin da aka datse wajen wasu ayyuka.
Fayemi ya faro wasu ayyuka na musamman a Ekiti wanda za a dade ana cin moriyarsu. A dalilin haka shi da na-kusa da shi su ka sadaukar da rabin albashinsu domin karasa ayyukan.
KU KARANTA: COVDI-19: Shugaban Gwamnonin Najeriya ya hangowa Jihohi fatara
Jawabin na kwamishinan watau Muyiwa Olumilua ya ce: “Tattakin arzikin Duniya ya gamu da cikas kuma hakan ya yi wa karfin tattalin Najeriya illa, wanda wannan ya taba jihar Ekiti.”
“A matsayinmu na gwamnati wanda ta san abin da ya kamata kuma mai daukar mataki, Fayemi ya duba kudin shiganmu bayan raguwar kason da ake samu daga gwamnatin tarayya.”
“Gami da raguwar kudin-shigan da mu ke samu daga haraji, wannan ya sa dole mu ka farka mu fuskanci halin da mu ka samu kanmu, duba tare da alkawarin da mu ka yi wa mutane.”
Gwamnan ya ce dole ya cika alkawuran da ya dauka a lokacin da ya ke neman kuri’a, ganin kuma nauyin da ke kansa na inganta halin rayuwar jama’a a wannan marra da aka shiga ciki.
“Wannan ragin albashi zai shafi gwamna, mataimakinsa da duk wani wanda mai rike da mukamin siyasa a gwamnati. Ba za a taba albashin ma’aikatan gwamnati ba.” Inji Olumilua.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng