Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu

Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu

An kara samun sabbin mutane 38 da suka kamu da cuta annobar Coronavirus mai toshe numfashi a jahar Kano, kamar yadda hukumar kare yaduwar cututtuka, NCDC ta bayyana.

NCDC ta bayyana haka ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter a daren Talata, inda tace jimillan masu dauke da cutar a Kano sun kai 115.

KU KARANTA: Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya

“An samu karin mutane 195 da suka kamu da cutar COVID19 a Najeriya kamar haka 80 – Lagos, 38 – Kano, 15 – Ogun, 15 – Bauchi, 11 – Borno, 10 – Gombe, 9 – Sokoto, 5 – Edo, 5 – Jigawa, 2 – Zamfara, 1 – Rivers, 1 – Enugu, 1 – Delta, 1 – FCT, 1 – Nasarawa.

“Zuwa karfe 11:50 na daren Talata 28 ga watan Afrilu, jimillan masu dauke da cutar a Najeriya sun kai 1532, mutane 255 sun warke yayin da mutane 44 suka rigamu gidan gaskiya.” Inji NCDC.

Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu
Adadin masu cutar Coronavirus a Kano sun kai 115 bayan samun mutane 38 da suka kamu
Asali: Facebook

A hannu guda kuma shugaban NCDC, Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa cibiyar gwajin cutar Coronavirus dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta cigaba da aiki a ranar Talata.

Dama dai cibiyar ta dakatar da aiki ne na tsawon kwanaki sakamakon feshi da aka mata. Haka zalika sabon cibiyar gwaji da jami’an Bayero ta bude zai fara aiki a ranar Laraba.

A wani labarin kuma, tsuguni bata kare ba, sakamakon an cigaba da samun mace macen jama’a da dama a jahar Kano ba tare da an san takamaimen abin da ke kashe su ba.

An sake tsintar gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya dake kofar Nassarawa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu.

Sai dai ba’a tabbatar da waye mamacin ba, amma hankulan jama’a sun tashi yayin da mutumin wanda shekarunsa sun kai sittin ya yanke jiki ya fadi a daidai kasar gadar, nan take ya mutu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa duk kokarin da suka yi na kiran jami’an tsaro da jami’an kiwon lafiya don dauke gawar mutumin ya ci tura, sakamakon sun ki amsa kiraye kirayen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel