Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya

Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya

Har yanzu tsuguni bata kare ba, sakamakon an cigaba da samun mace macen jama’a da dama a jahar Kano ba tare da an san takamaimen abin da ke kashe su ba.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito an sake tsintar gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya dake kofar Nassarawa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai ma Yansanda harin kwantan bauna a Kaduna, sun kashe 1, saura sun jikkata

Sai dai ba’a tabbatar da wanene mamacin ba, amma hankulan jama’a sun tashi yayin da mutumin wanda shekarunsa sun kai sittin ya yanke jiki ya mutu a daidai kasar gadar.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa duk kokarin da suka yi na kiran jami’an tsaro da jami’an kiwon lafiya don dauke gawar mutumin ya ci tura.

Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya

Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya
Source: Facebook

“Hankulanmu sun tashi, ba mu san abinda ya kashe shi ba, mun dai tsinci gawarsa kwance a kasa, mun kira ma’aikatar kiwon lafiya da Yansanda tun da rana, amma babu wani bayani daga wajensu, a yanzu har gawar ta fara kumbura.” Inji shi.

Daga inda wannan lamari ya auku zuwa ofishin hukumar kwana kwana ta jahar Kano bai wuce tazarar mita 100 ba, amma ta gagara aika jami’anta don su ga abin dake faruwa a wurin.

Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne aka yi ta samun mace mace a jahar Kano ba tare da sanin sababin mutuwar jama’an ba, zuwa yanzu fiye da mutane 200 sun mutu a jahar.

Sai dai wasu jama’an jahar da masana kiwon lafiya na danganta mace macen da yaduwar annobar Coronavirus mai toshe numfashi, wanda a yanzu ta kashe akalla mutane 40 a Najeriya.

Amma gwamnatin jahar Kano ta bakin kwamishinan watsa labarunta, Muhammad Garba ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen da aka dinga samu a jahar a makon da ta gabata.

A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.

Kwamishinan ya ce sun gano haka ne bayan gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel