Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4

A cikin kwanaki hudu tak ne jihar Kano ta yi rashin manyan sanannun mutane da suka hada da malaman jami'a, kwaleji, Islama da kuma ma'aikatu.

Rashin manyan mutanen ya zo ne a lokacin da ake korafi a kan yawan mace-macen masu tada hankulan jama'a a jihar.

Duk da cewa lamarin na aukuwa ne a daidai lokacin da annobar Korona ta gallabi duniya, babu tabbacin da ke nuna cewa cutar ce ta kashe mutanen.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

A ranakun karshen mako ne aka samu mace-macen da suka kwashe wadannan sanannun mutanen.

Mutuwar wadannan bayin Allah ta janyo alhini da jimami a shafukan sada zumuntar zamani.

Ga bayani da hotunan wadannan sanannun mutanen.

Farfesa Ibrahim Ayagi

Ya rasu a ranar Asabar 25 ga watan Afirilun 2020. Iyalansa sun sanar da cewa ya rasu ne bayan rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

Farfesa Aliyu Umar Dikko

An haifeshi ne a shekarar 1953 kuma ya rasu yana da shekaru 67 a duniya.

Ya mutu ya bar mata daya da 'ya'ya bakwai da jikoki bakwai.

Farfesa Balarabe Maikaba

Ya rasu a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilu bayan fama da ya yi da zazzabi na 'yan kwanaki.

Ya rasu ya bar mata hudu da 'ya'ya 16.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

Dr. Sabo Kurawa

Ya rasu a ranar 26 ga watan Afirilun 2020 duk da iyalansa sun tabbatar da cewa bashi da lafiya.

Ya rasu ya bar mace daya, Farfesa Dijeh Kurawa da yara shida.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

Dr Uba Adamu

Dakta Muhammad Uba Adamu ya rasu ne a ranar Litinin 27 ga watan Afirilun 2020. Iyalansa sun ce bai yi tafiya zuwa wata kasa ba a baya-bayan nan.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

Dr Ghali Kabeer Umar

Ya rasu a ranar Litinin kuma shine shugaban jami'ar fasaha ta Wudil Kano.

Har a halin yanzu ba a san musabbabin mutuwarsa ba.

Ustaz Dahiru Rabiu

Shine tsohon alkalin alkalai na jihar Kano.

Malamin addinin Islaman ya rasu ne sakamakon zazzafan zazzabi da ya yi fama dashi..

Abdullahi Lawal

Kafin rasuwarsa, shine shugaban yanki na bankin First Bank a Kano.

Ana zargin cutar coronavirus ce ta kashe shi.

Kafin nan, zazzafan zazzabi hadi da tari sai sarkewar numfashi ne suka addabeshi. An mika shi asibiti amma ya rasu a ranar Asabar.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

Musa Ahmad Tijjani

Tsohon ma'aikacin jarida ne kuma editan jaridar Leadership Sunday.

Ya rasu ne sakamakon zazzabin da yasa aka kwantar da shi a asibiti na tsawon mako guda.

Sheikh Tijjani Tukur Yola

Fitaccen Malamin addinin Musulunci ne na darikar Tijjaniya.

Ya rasu a ranar Litinin 27 ga watan Afirilun 2020.

Hajiya Halima Shitu

Malama Halima mata ce ga fitaccen malami Sheikh Abdulwahab Abdullahi.

Tana daya daga cikin tsirarun mata malamai a Kano kuma ita ce macen da ta fara tafsiri cikin malamai mata.

An haifeta a unguwar Yakasai. Yayarta ta tabbatar da cewa ta rasu ne bayan zazzafan zazzabi na kwanaki hudu.

Ta rasu ta bar yara shida a duniya.

Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel